Kotu ta sake tura Nawaz Sharif, na Pakistan gidan yari

Daruruwan magoya bayan Nawaz Sharif sun mamaye harabar kotun Islamabad

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Daruruwan magoya bayan Nawaz Sharif sun mamaye harabar kotun Islamabad

Kotu ta sake yanke wa tsohon Firaaministan Pakistan Nawaz Sharif hukuncin dauri kan wata sabuwar tuhumar aikata almundahana.

Kotun yaki da cin hanci da rashawa a Islamabad ta daure Sharif, shekaru bakwai a gidan gidan kan yadda jarinsa ya haura asalin kadarorin da ya mallaka.

Mista Sharif wanda ya sha musanta aikata ba daidai, an taba daure shi a watan Yuli kan wata shari'a ta daban amma aka ba da shi beli bayan wata babbar kotu a Islamabad ta dakatar da hukuncin a watan Satumba.

Jam'iyyarsa ta sha kaye a zaben watan Yuli bayan an daure shi.

Nawaz Sharif ya kasance Firaministan Pakistan daga ranar 5 ga watan Yuni 2013 zuwa 28 ga watan Yulin 2017.

Nawaz Sharif ya yi murabus ne bayan alkalin kotun kolin Pakistan ya sauke shi daga mukaminsa.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan wani bincike da aka yi kan dukiyar iyalinsa sakamakon abin kunyar nan na Panama Papers ya gano cewa yana da dukiya a kasashen da ke kaucewa biyan haraji.

Bayan yanke masa sabon hukuncin, jam'iyyarsa ta Muslim League-Nawaz ta yi barazanar kaddamar da zanga-zanga tare da dagula lamurran majalisa idan har aka sake tura shugabanta gidan yari.

Jami'an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa magoya bayansa a harabar kotun.

Sharif ya ce siyasa ce kawai kan shari'ar da ake masa, inda ake sa ran zai daukaka kara.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An girke Jami'an tsaro da dama a harabar kotu