Gwamnar Puebla a Mexico ta mutu a hadarin jirgin sama

Martha Erika Alonso speaks during her swearing-in ceremony in Puebla state, Mexico. Photo: 14 December 2018

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranar 14 ga wannan watan aka rantsar da Martha Erika Alonso ga mukamin gwamnar Puebla

Gwamnar jihar Puebla da ke tsakiyar kasar Mexico, Martha Erika Alonso ta mutu a wani hadarin jirgin sama, kwanaki kadan bayan an rantsar da ita ga mukamin.

Mijinta Sanata Rafael Moreno Valle ma ya mutu.

Rahotanni daga Mexico na cewa hadarin ya auku ne jim kadan bayan da jirgin saman da suka shiga ya tashi dagabirnin Puebla.

Uwargida Alonso mai shekara 45 ta kasance mace ta farko da ta taba rike mukamin gwamna a jihar Puebla bayan ta yi takara da ke cike da takaddama da abokin karawarta.

Ita mamba ce ta jam'iyyar PAN.

Sabon shugaban kasar Mexico Andrés Manuel López Obrador ya tabbatar da mutuwar ta.

Ba a tabbatar ko matukin jirgin ya tsira da ransa ba, a hadarin da ya auku a kusa da babban birnin jihar Puebla, wanda kuma shi ne birni na biyu a girma a fadin kasar.

Ranar 14 ga wannan watan ne Misis Alonso ta lashe zaben zama gwamna bayan da ta doke dan takarar da shugaban kasa mai ci ke mara wa baya.

A baya mijinta ya taba zama gwamnan jihar ta Puebla.

Wannan hadarin ya biyo bayan wasu hadurran na jirgi mai saukan ungulu a kasar ta Mexico, wanda ya hada da na ministan cikin gida Francisco Blake Mora a 2011.

A farkon wannan shekarar ma mutum 13 sun halaka a yayin da wani helikwafta ya fado kan jama'a, amma ministan da ke cikin jirgin bai mutu ba.