MTN ya biya Najeriya kimanin N20bn

Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka, MTN

Asalin hoton, Reuters

Kamfanin sadarwa na MTN ya sasanta da babban bankin Najeriya, inda ya amince ya biya wasu kudade kasa sosai da yadda aka yi tsammani.

Babban bankin ya umarci kamfanin na Afirka Ta Kudu ya mayar da dala biliyan takwas da hukumomi suka ce ya fitar daga Najeriya ba bisa ka'ida ba.

Sai dai bayan kwashe tsawon watanni ana kwan-gaba kwan-baya, daga bisani bangarorin biyu sun amince da biyan dala miliyan 53 kwatankwacin naira biliyan 20 kasa da kashi 1% na tarar da aka yi masa tun farko.

A cikin wata sanarwa, kamfanin MTN ya ce babban bankin Najeriya ya yi bitar karin wasu bayanai kafin ya yanke shawarar cewa ba sai ya biya tarar farkon ba.

Dala miliyan 53 ta shafi wata hada-hadar kudi dala biliyan daya da MTN ya yi ne a shekara ta 2008, wadda babban bankin ya ce an yi abin ba tare da samun amincewar karshe ba.

Sai dai, har yanzu, kamfanin na ci gaba da shari'ah da gwamnatin kasar kan harajin dala biliyan biyu da atoni janar din Najeriya ya ce sai ya biya a watan Satumba.