Bidiyon yadda Buhari ya rera wakar Kirsimeti

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa da kuma shugaban APC

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Buhari ya taya 'yan Najeriya murnar Kirsimeti

Shugaban Muhammadu Buhari ya taya kiristocin Najeriya murnar bikin kirsimeti ta hanyar rera waka.

A wani hoton bidiyo da shugaban ya wallafa a shafin shi na Twitter, an ga Buhari ya rera wakar Kirsimeti tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a kuma shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.

Sun rera wakar a tsaye Buhari yana tsakiya cikin murna da murmushi da juna.

Baya ga bidiyon da ya wallafa a Twitter, shugaba Buhari kuma ya taya 'yan Najeriya murnar bikin Kirsimeti.

A cikin sakon ya ce, "Kirisimeti biki ne na tunawa da haihuwar Yesu a birnin Bayt Lahm shekaru aru-aru; da kuma sako na fatan ceto da gafara da tausayi da zaman lafiya da Yesu Almasihu ya gabatar."

Bidiyon ya samu tsokaci kusan 1,000 inda shugaba Buhari ya sha yabo da suka.

Wasu sun ji dadin sakon na taya murna, yayin da wasu kuma suka ce siyasa ce kawai saboda zabe na karatowa, domin shekaru uku a baya na mulkinsa ba su ga shugaban yana rera wakar kirsimeti ba.