Bambanci ba illa ba ne arziki ne - Fafaroma Francis

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Fafaroma Francis ya jaddada bukatar nuna kauna tsakanin al'umma na kowace kasa da kuma kowane addini suke bi, a cikin sakon da ya saba gabatarwa na Kirsimeti.

A sakon da ya karanta a dandalin St Peter a gaban dimbin mabiya, ya ce bambance bambance da ake da su ba illa ba ne, arziki ne.

Fafaroma da ke jagorantar darikar Katolika ta mabiya sama da miliyan 1.3 ya yi kira ga Syria da ta tuna 'yan uwantakar da ke tsakanin al'umarta bayan shafe shekaru ana yaki.

Fafaroma ya kuma yi fatan tsagaita wutar da aka cinma a Yemen zai kawo sauki ga wadanda yaki da yunwa suka jefa su cikin yanayi na galabaita.

Ya kuma yi fatan za a ake farfado da tattauna zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa domin kawo karshen yaki tsakaninsu.

Haka nan ya yi tsokaci kan miliyoyin 'yan gudun hijirar Afrika da ke bukatar taimako, tare da fatan kyautatuwar dangantakar da aka samu a yankin Koriya za ta kara karfi.