Hotunan yadda aka yi bikin Kirsimeti a duniya

An gudanar da tarukan ibada na Kirsimeti a kasashe daban-daban na duniya domin tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.

Ga wasu hotuna da muka zabo kan yadda aka yi bukukuwan Kirsimetin.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Ranar jajiberen Kirsimeti an yi addu'o'i a fadar Vatican, inda Fafaroma Francis ya bukaci mabiya su kasance masu "rarrabawa da kuma bayar da abin hannunsu", sannan ya yi tur da masu kankamo

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A Masar, wannan yarinyar na sauraren hudubar da aka yi a wani Coci da ke birnin Alkahira.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An gudanar da addu'o'i a wani Coci da ke Fuyang a lardin Anhui na gabashin China

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kiristocin kasar India na cikin wadanda suka yi addu'o'i a wani Coci da ke birnin Bangalore

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan matar ta yi addu'a a Cocin the Sacred Heart Cathedral da ke birnin Lahore na kasar Pakistan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Masu ibada sun yi jerin gwano a wannan coci da ke birnin Bangkok domin taba jaririn da aka yi wa lakabi da Yesu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wadannan matasan na cikin mutanen da suka yi addu'o'i a wani Cocin Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan yaron na cikin dubban 'yanb gudun hijira wadanda ke kan hanyarsu daga Kasashen Tsakiyar Amurka zuwa Amurka amma suka gudanar da bikin Kirsimeti a Tijuana, Mexico

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar jajiberen Kirsimeti an gudanar da addu'o'i a Surabaya, birni na biyu mafi girma a Indonesia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mambobin kungiyar nunkaya ta birnin Berlin sun bi sahun mabiya addinin Kirista da suka yi wanka a kofin Orankesee don bikin Kirsimeti

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wannan matar ta sumbaci mijinta a kusa da wata bishiyar Kirsimeti a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu iyalai sun je gefen tekun Bendi da ke Sydney domin debe kewa lokacin bikin Kirsimeti

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mabiya addinin Kirista sun halarci taron addu'o'i a Cocin Santa Maria ta Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

A Faransa, masu zanga-zangar nan da ke sanye da shudayen riguna sun gudanar da addu'o'i a wata mahadar hanya da ke birnin Somain na arewacin kasar.

All photographs belong to the copyright holders as marked.