Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji 13 a Maiduguri

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojoji 13 da dan sanda daya ne suka hallaka sanadiyyar wani kwantan-bauna da mayakan Boko Haram suka yi musu a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
Al'amarin, a cewar wata sanarwa daga dakaru masu yaki da kungiyar Boko Haram ta hannun Kanar Onyema Chukwu, ya faru ne a ranar Litinin.
A cewarta, sojojin na runduna ta daya, sun yi musayar wuta tare da tsallake tarkon da mayakan, wadanda ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kafa masu.
Baya ga haka kuma dakarun sun ce sun samu nasarar dakile wani hari da kungiyar ta Boko Haram ta kai wa sojoji a sansaninta da ke Kukareta, da ke a karamar hukumar Damaturu a jihar Yobe.
Rundunar ta ce ta kashe mayakan da dama, sai dai soja daya ya rasa ransa.
A baya-bayan nan dai mayakan Boko Haram na kara kaimi wajen kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Abinda ya sanya shugabannin kasashe na yankin Chadi suka yi taro domin nemo sabuwar dubarar da za su yi amfani da ita wajen tunkarar mayakan.