Yadda Hosni Mubarak ya bada sheda a shari'ar Mohamed Morsi

Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak

Asalin hoton, Reuters

Tsoffin shugabannin Masar biyu Hosni Mubarak da Mohamed Morsi za su yi ido da ido a kotu a karon farko.

Hosni Mubarak mai shekara kusan 90 ya bada shaida ne a shari'ar da ake sake yi wa wanda ya gaje shi Mohamed Morsi da sauran shugabannin kungiyar 'yan Uwa Musulmi.

Ana zargin 'yan kungiyar da haddasa bore da bude gidajen yari fursunoni su tsere a lokacin tarzomar kasashen Larabawa ta 2011.

Da ma dai wata kotu a Alkahira ta taba yanke wa Morsi hukuncin kisa amma sai wata kotun daukaka kara ta soke hukuncin a 2016.

Mista Mubarak ya shaida wa kotun cewa ya samu bayanai a lokacin da ke cewa daruruwan mayaka sun shiga Masar ta hanyar wani mashigi daga Gaza.

A ranar 25 ga watan Janiru ne ake cika shekara takwas da kaddamar juyin juya hali a Masar wanda ya yi sanadin kawo karshen mulkin Hosni Mubarak wanda ya shafe shekaru da dama yana mulki a kasar.

Yadda Mubarak ya bada sheda

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Reuters