Da gaske 'yan sandan Najeriya sun tsere daga yaki da Boko Haram?

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa jami'anta sun tsere daga arewa maso gabashin kasar inda ake yaki da Boko Haram.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Jimoh Moshood ya aike wa manema labarai ta ce dukkan jami'an nata 2000 na can yankin suna aikin da aka tura su yi.

Wata jaridar da ake wallafawa a shafin intanet Premium Times ce ta yi zargin cewa jami'an 'yan sanda 167 sun tsere daga fagen daga.

"Wannan labari karya ce tsagwaronta kuma yunkuri ne na yin tarnaki kan jajircewar da 'yan sanda ke yi wurin yakin da mayakan Boko Haram", in ji mai magana da yawun rundunar 'yan sandan.

Da ma dai an tura jami'an ne domin su hada gwiwa da sojoji wurin fatattakar 'yan Boko Haram.

Mayakan na Boko Haram sun matsa kai hare-hare a baya bayan nan, inda ko da a farkon makon nan sai da suka kashe sojoji 13 da 'yan sanda biyu a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Asalin hoton, NPF