Trump ya ziyarci dakarun Amurka da ke Iraqi

Mr Trump da mai dakinsa sun gana da dakarun kasar ne a sansanin sojin sama na al-Asad da ke yammacin Bagadaza

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Trump da mai dakinsa sun gana da dakarun kasar ne a sansanin sojin sama na al-Asad da ke yammacin Bagadaza

Shugaban Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania Trump sun kai ziyarar ba-zata Iraqi inda suka yi wa dakarun kasarsu barka da kirsimeti.

Fadar White House ta ce sun je kasar ne "da tsakar daren ranar kirsimeti" domin su gode wa dakarun kasar "bisa aikin da suke yi da gudunmawar da suka bayar da kuma nasarar da suka samu."

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Mr Trump na cewa Amurka ba ta da shirin janye dakarunta daga Iraqi.

Ziyarar ta zo ne kwanaki kadan bayan sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya ajiye aiki saboda rashin jituwa game da tsare-tsaren gwamnati kan yankin gabas ta tsakiya.

Mr Trump da mai dakinsa sun shiga jirgin Air Force One zuwa sansanin sojin sama na al-Asad da ke yammacin Bagadaza, babban birnin kasar inda suka gana da jami'an soji a dakin cin abinci na sansanin.

Wannan shi ne karon farko da ya kai ziyara yankin.

Shugaba Trump ya tsara gudanar da bikin kirsimetinsa ne a Florida, sai dai ya yi zaman sa a Washington saboda matsalar dakatar da ayyukan wasu ma'aikatun gwamnati.

Amurka na da dakaru kusan 5,000 a Iraqi wadanda ke tallafa wa gwamnatin kasar wurin yaki da mayakan kungiyar IS.