An fi haihuwar maza fiye da mata a wasu sassan duniya

Wasu kasashen sun fi son samun ya'ya maza fiye da mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu kasashen sun fi son samun ya'ya maza fiye da mata

Tun lokacin da aka fara adana alkalumma a 1838, mafi yawan ya'yan da ake haihuwa maza ne.

Tun hawan Sarauniya Victoria, ba a taba samun ko da shekara guda da haihuwar 'ya'ya mata ya kere na maza ba a Ingila.

Misali, a shekarar 2017 a Ingila da Wales an samu haihuwar maza 348,071 da kuma mata 331,035 wato ratar maza 17,000.

Kuma wannan shi ne irin ratar da ake samu a kowace shekara ko ma fiye tun kimanin shekara 180 da suka wuce.

Ana samun haihuwar maza 105 a cikin kowacce haihuwar mata 100.

Kusan duk haka yake a ko'ina a fadin duniya, duk da cewa a wasu kasashen kamar China da Indiya, ratar ta fi haka saboda an fi muradin samun ya'ya maza.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mata sun fi yiyuwar dadewa a duniya a cewa wani bincike

Ko me ya sa?

Masana na ganin cewa hakan ba ya rasa nasaba da farkon halittar dan Adam.

A ganinsu, kafin a samu daidaito a adadin maza da mata, dole sai an haifi jarirai maza fiye da mata.

Sun ce kasancewa namiji abu ne mai hadari.

Farfesan kidaya na jami'ar Oxford, David Steinsaltz ya bayyana cewa akwai yiwuwar maza suna iya mutuwa fiye da mata a yarinta da kuma ko wani mataki na rayuwarsu dalilin hadurra ko rashin lafiya.

Wasu dalilan kuma sun hada da shekarun iyaye, da irin abincin da suke ci, da yanayin hutawarsu, da yanayin jikin mahaifiyar wato idan jinin al'ada ya dade ya yanke mata ko a'a.

Haka kuma, wasu masana na ganin cewa, akwai yiwuwar samun 'ya mace idan iyayen suka sadu kwanaki kadan bayan jinin al'ada ya dauke wa mahaifiyar.