Shin Boko Haram ta kori sojoji ta kwace garin Baga?

Mayakan sun kafa tutarsu a gaban wani masallaci a cikin garin Baga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mayakan sun kafa tutarsu a gaban wani masallaci a cikin garin Baga

Rahotanni daga Baga da ke jihar Barno a arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun shiga garin inda suka kara da sojojin Najeriya.

Wasu bayanai na cewa mayakan sun kafa tuta a garin na Baga bayan sun shafe daren Laraba suna fafatwa da sojoji da ke garin.

Wani mazaunin gairn da ya shaida lamarin yace 'yan Boko Haram din sune ke iko da garin, domin sun kafa tuta, sannan babu wani soja ko da ya da ya rage a cikin garin.

Ya bayyana wa BBC cewa mayakan sun afkawa wani babban sansanin soji da ke gefen ruwa a garin na Baga.

To sai dai kakakin rundunar sojan kasa ta Najeriya Janar Sani Kukasheka Usman ya ce Boko Haram ba ta kwace garin ba, amma suna ci gaba da wani aiki a garin, kuma nan gaba za su yi karin bayani kan halin da ake ciki.

Rundunar sojin Najeriya dai ta sanar cewa mayakan Boko Haram sun kai hari shelkwatar dakarun gamayya na kasashen yankin tafkin Chadi ne da ke Baga a jiya Laraba.

Ta ce dakarunta sun yi fada kan jiki kan karfi don korar mayakan Boko haram din, kuma daya daga cikin sojojin ya rasa ransa a yayin fadan.

Sai dai wanda ya shaida lamarin ya ce mayakan sun shiga garin na Baga bayan wasu daga cikinsu sun yi wa sansanin sojojin kawanya.

Ya kuma ce sojojin da ke cikin garin Baga sun tsere zuwa Munguno.

Ya bayyana cewa mayakan sun kafa tutarsu a babban masallacin Juma'a na garin Baga, kuma 'yan bindigan ne ma suka ja sallar Asuba.

"Muna isa masallaci sai muka ga mutane rike da bindigogi", a cewarsa.

Ya ce 'yan bindigan sun yi wa jama'ar garin bayanin cewa su mayakan Boko Haram ne na bangaren Mamman Nur kuma babu ruwansu da dukiyar talaka ko kashe mutane.

"Sun ce su 'yan kungiyar IS ne, kuma sun ce mu kwantar da hankalinmu", in ji shi.

A halin yanzu dai, mutumin ya ce ya tsere Maiduguri kuma bai fuskanci wani tashin hankali ba daga gurin 'yan bindigan duk da cewa a idonsu ya fita ya bar garin.

Rundunar Sojin Najeriya dai ta ce mayakan Boko Haram din na buya a garin Baga da kewaye kuma dakarunta na kokarin gano su.

Rundunar ta kuma ce an tura karin sojojin ruwa da na kasa don samun karin karfin korar 'yan ta'addan.