Kalli wasu zababbun hotuna masu kayatarwa daga sassan duniya

Mun zabar maku wasu hotuna masu matukar kayatarwa da aka dauka daga sassan duniya daban daban a shekarar da ta wuce.

Wani shudin Filfilo a kan fuskar wata mai tallan kayan kawa, Jessie Baker, a lambun Wisley da ke garin Surrey.

Asalin hoton, Jack Taylor / Getty Images

Bayanan hoto,

Wani shudin Filfilo a kan fuskar wata mai tallan kayan kawa, Jessie Baker, a lambun Wisley da ke garin Surrey.

Asalin hoton, Jane Barlow / PA

Bayanan hoto,

Wasu mambobin Junior Jarl Squad dauke da sanduna da wuta ke ci a jikinsu a tsibirin Shetlan Isles, lokacin wani bikin gargajiya na UP Helly Aa Vikings da ake gudanarwa duk shekara ran Talatar karshe a duk watan Janairu.

Asalin hoton, Owen Humphreys / PA

Bayanan hoto,

Mutane na tafiya tare karnukansu a gabar teku na Blyth a Northnumberlamnd, bayan da dusar kankara ta lullube wasu sassan kasar

Asalin hoton, Victoria Jones / PA

Bayanan hoto,

Stormzy yana wasa a gaban jama'a a wajen bikin bayar da lambar girma na Brit 2018 a filin wasa na O2 Arena a kudu maso gabashin Landan ran 20 ga Fabrairu 2018

Asalin hoton, BEN STANSALL / AFP

Bayanan hoto,

Ma'aikatan agaji na gyara wani tanti inda aka ga Segei da Yulia Skripal a cikin mawuyacin hali a wani katon kanti a Salisbury a ranar 4 ga watan Maris. 'Yan sanda dai sun zargi cewa an kai wa dan leken asirin da 'yarsa hari ne da wani guba mai suna Novichock.

Asalin hoton, Charles McQuillan / Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu sun shiga bikin yaba tabo na shekara-shekara a garin Portdawon, Co Armagh da ke Ireland.

Asalin hoton, Chris Jackson / Getty Images

Bayanan hoto,

Matar Yarima Charles yayin da take barin asibitin St Mary a Landan, bayan ta haifi Yarima Louis. An haife shi ne ranar 23 ga watan Afrilu da karfe sha daya kuma shi ne na biyar a jerin masu jiran gado na masarautar Ingila.

Asalin hoton, ADRIAN DENNIS / AFP

Bayanan hoto,

Mutum-mutumin Millicent Fawcett, wata mai fafutukar kare hakkin mata ke nan aka kafa a gaban majalisar Birtaniya a tsakiyar birnin Landan. Mutum-mutumin na bikin cika shekara 100 ne tun kaddamar da dokar da ta bai wa mata 'yan sama da shekara 30 damar yin zabe.

Asalin hoton, AARON CHOWN / AFP

Bayanan hoto,

Yarima Harry tare da matarsa Meghan lokacin da suke goye a kan doki, suna wucewa ta gaban jama'a bayan an daura masu aure a fadar Windsor a Berkshire. Dubban mutane sun tsaya a bakin titi domin su ga wucewarsu.

Asalin hoton, Jeff J Mitchell / Getty Images

Bayanan hoto,

Minista Nicola Sturgeon ta hau lilo a lokacin bude filin wasan yara a Dunfemline. An gyara filin wasan ne domin yara masu nakasa da ma wadanda ba su da ita.

Asalin hoton, Anthony Devlin / Getty Images

Bayanan hoto,

Wata ya fito a yyain da wutar daji ke ruruwa kusa da Buckton Vale a Greater Manchester. Wutar ta barke ne ran 24 ga Yuni kuma kusan sojoji 100 aka aika domin dakushe ta.

Asalin hoton, Ministry of Defence via Getty Images

Bayanan hoto,

Jiragen Red Arrows suna wasa a sararin samaniya a Landa a watan Yuli. An gudanar da wani Fareti da wasa da jirage 100 wadanda su ka bi saman gidan sarauniya domin bikin murnar cika shekara 100 da kafa sojojin sama na kasar.

Asalin hoton, Stefan Rousseau / PA

Bayanan hoto,

Shugaban Amurka Donald Trump, tare da Firaministar Birtaniya, Theresa May a gidanta dake Chequers, lokacin da ya kai ziyara a Birtaniya.

Asalin hoton, Toby Melville / Reuters

Bayanan hoto,

Jami'an lafiya na duba wata agwagwa a lokacin bikin duba tsuntsayen sarauniya wanda ake kira da Swan-upping a bakin rafin Thames a Surrey.

Asalin hoton, Ian MacNicol / Getty Images

Bayanan hoto,

Tawagar Sifaniya kenan suke jujjuyawa a wasan iyo na ruwa a lokacin wasan karshe na gasar Glasgow 2018 na zakarun Turai.

Asalin hoton, Hannah McKay / REUTERS

Bayanan hoto,

Mai sha'awar kwalliya Sophie Cochevelou a taron makon kwalliya na Landan.

Asalin hoton, Jeff J Mitchell / Getty Images

Bayanan hoto,

Firaminista Theresa May na rawa a gaban jama'a yayin gabatar da jawabinta a ranar karshe na taron Jam'iyyar Conservative Party a Birmingham a watan Oktoba.

Asalin hoton, PAUL ELLIS / AFP

Bayanan hoto,

Shugabannin addinin Buddha suna addu'o'i a gaban hoton Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, Vichai Srivaddhanaprabha, a wajen filin wasa na King Power. Attajirin dan kasuwan na daga cikin mutane biyar da jirgi mai saukar angulu ya kashe lokacin da ya fadi kuma ya kone a filin wasan jim kadan bayan tashinsa.

Asalin hoton, Kirsty O'Connor / PA

Bayanan hoto,

Kyaftin James Pugh yana sanya wata alama cikin alamomin da mawaki Rob Heards ya sanya domin girmama gwarazan yakin duniya na daya a lambun Sarauniya Elizebeth a gabashin Landan. Cikin 'yan agaji har da mambobin Royal Anglian na daya, wanda aka sanya alamomi 72,396, alamomin na nuni ga sojojin da ba a samu gawarwakinsu ba.

Asalin hoton, Leon Neal / Getty Images

Bayanan hoto,

Masu shigar mutum-mutumi wadanda suke wakiltar Dream and Wishes ke fitowa daga ofishin Firaminista na 10 Downing Street.