An koka kan sabon tsarin Instagram

Mutane sun yi Allah wadai da gyaran

Asalin hoton, INSTAGRAM

Bayanan hoto,

Mutane sun yi Allah wadai da gyaran

Instagram ya nemi afuwa daga jama'a bayan da kamfanin ya fitar da wani sabon tsarin shafin ga miliyoyin masu amfani da shi.

Sabon tsarin dai ya kunshi matsar da hotuna gefe maimakon daga sama zuwa kasa.

Jim kadan bayan fitar da sabon tsarin, masu amfani da shafin suka garzaya shafin Twitter inda suka rika sukar sabon tsarin tare da neman a maido masu da wancan da suka saba amfani da shi.

Sabon tsarin dai bai wuce sa'a daya ba kafin Instagram din ya yi hanzarin cire shi.

Shugaban sashen kula da kayyaki na Instagram, Adam Mosseri ya wallafa bayani a shafinsa na Twitter, inda ya ce "Muna neman afuwa a kan wannan, wannan wani dan karamin gyara ne muka so muyi, amma sai wuce fiye da yadda muke tunani."

"Amma yanzu mun dawo da tsarin da kuka sani. Idan har yanzu kuna ganin sabon tsarin sai ku kashe wayar ku sannan ku sake kunnawa za ku ga komai ya gyaryu" a cewar Mosseri.