Tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari ya rasu

Shehu Usman Aliyu Shagari

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto,

Shehu Usman Aliyu Shagari ya rasu ne yana da shekara 93 a duniya

Bayanan da muka samu daga iyalan tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya rasu ranar Juma'ar nan. Tshohon shugaban ya rasu ne a asibitin kasa da ke Abuja inda yake jinya

Alhaji Shehu Shagari ya rasu yana da shekara 93 a duniya, bayan ya sha fama da jinya.

Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983, lokacin da sojoji suka yi gwamnatinsa ta jamhuriya ta biyu juyin mulki, inda Janar Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa.

Alhaji Shehu Shagari yana cikin 'yan siyasar jamhuriya ta farko, da suka yi ministoci a gwamnatin Tafawa Balewa tsakanin 1960 zuwa 1966 da sojoji suka yi wa gwamnatin juyin mulki.

Ya rasu ya bar 'ya'ya 19, maza takwas mata 11 da jikoki da dama.

Gabanin rasuwarsa ya rike sarautar Turakin Sakkwato, wanda babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Sarkin Musulmi.

Ya rike wannan sarauta tun daga 1962 har zuwa rasuwarsa.

An garzaya da shi zuwa asibiti a Abuja ne bayan da jikinsa ya yi tsanani a ranar Talata.

Alhaji Shehu Shagari ya sha fama da ciwon Limoniya.

Ana sa ran za a mayar da shi Sakkwato ranar Asabar domin yi masa jana'iza.