Sojoji sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta murkushe hare-haren mayakan Boko Haram a garin Baga na jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Ibekunle Daramola ya fitar, ta ce bayan harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar kan sojojin kasar, rundunar ta aika da jiragen yaki da suka fatattaki mayakan.

A washegarin kirsimeti ne mayakan Boko Haram suka shiga garin Baga suka yi musayar wuta da na sojojin Najeriya inda wasu rahotanni suka ce har kwace ikon garin tare da kafa tuta.

Sai dai a sanarwar da rundunar sojin ta fitar mai dauke da hoton bidiyo ta ce jiragen yaki da suka hada da masu saukar angulu sun kai wa sojojin dauki inda kuma suka fafattake su daga garin na Baga.

Wasu bayanai na cewa mayakan sun kafa tuta a garin na Baga bayan sun shafe daren Laraba suna fafatwa da sojoji da ke garin.

Wani mazaunin gairn da ya shaida lamarin yace 'yan Boko Haram din sune ke iko da garin, domin sun kafa tuta, sannan babu wani soja ko da ya da ya rage a cikin garin.

Ya bayyana wa BBC cewa mayakan sun afkawa wani babban sansanin soji da ke gefen ruwa a garin na Baga.

Rundunar Sojin Najeriya dai ta ce mayakan Boko Haram din na buya a garin Baga da kewaye kuma dakarunta na kokarin gano su.

Rundunar ta kuma ce an tura karin sojojin ruwa da na kasa don samun karin karfin korar 'yan ta'addan.