Kalli bidiyon kabarin marigayi Shehu Shagari

Kalli bidiyon kabarin marigayi Shehu Shagari

Danna alamar lasifika a sama domin kallon bidiyon kabarin Marigayi Shagari

Alhaji Shehu Aliyu Shagari, shugaba na farko mai cikakken iko ya rasu ne a ranar Juma'a 28 ga watan Disamban 2018

Tsohon shugaban ya rasu ne a asibitin kasa da ke Abuja inda yake jinya.

An binne shi a a mahaifarsa garin Shagari.

Alhaji Shehu Shagari ya rasu yana da shekara 93 a duniya, bayan ya fama da jinya.

A mahaifarsa garin Shagari aka yi wa gawar tsohon shugaban na Najeriya Sallar Jana'iza inda kuma a nan ne za a binne shi.

Yadda aka yi jana'izar Shehu Shagari

An fara sallar jana'izarsa ne da misalin karfe uku na rana a gidansa da ke Shagari.

Dubban ma su alhini ni ne daga sassa daban-daban suka yi wa gawar addu'a a yayin sallar ta tsawon mintuna biyu.

Daga cikinsu akwai tawagar gwamnatin kasar wadda ta kunshi ministoci da kuma sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha wanda ya jagorance ta.

Haka ma gwamnonin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara na daga cikin wadanda suka halarci jana'izar.

Daga nan aka dauki gawar domin binne ta a wani kabari da aka haka a wani bangare na katafaren gidansa a yayin 'ya'ya da jikokin da makusanta ke sharbar hawaye.

Lokaci ne dai mai sosa rai ga wanda ya gani.

Bayan da aka kammala binne gawar tsohon shugaban wata tawagar sojojin kasar ta zagaye kabarin domin yi bankwanan ban-girma.

Sun yi harbi sau ukku a sama zagaye da kabari tsohon shugaban wanda ya shugabanci kasar a shekarun 1979 zuwa 83.

Daruruwan mutane ne suka halarci sallar jana'izar a garin Shagari.