'Yan sandan Masar sun 'kashe 'yan ta'adda 40'

The raids came hours after a tourist bus was hit by a roadside bomb near the Giza pyramids

Asalin hoton, Getty Images

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Masar ta ce mutanen na shirin kai wani jerin hare-hare ne akan wuraren yawon bude idanu da majami'ai da sansanonin sojojin kasar.

Wannan ya biyo bayan wani harin bam da aka kai ranar Juma'a kan wata motar bas da ke dauke da 'yan yawon bude idanu a Giza.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu 'yan Vietnam uku masu yawon bude idanu da kuma wani dan Masar daya, amma masu tsautsauran ra'ayi sun sha kai irin wannan harin akan cibiyoyi irin wannan a cikin kasar a shekaun baya.

A lokacin harin, 'yan sanda sun kashe mayaka 30 a yankin na Giza, inda suka kashe mahara 10 kuma a El-Arish, wanda shi ne babban binin lardin Arewacin Sinai.

An dai tsaurara matakan tsaro a Masar musamman a wannan lokaci da Kibdawa mabiya addinin Kirista na kasar ke shirin gudanar da bikin Kirsimati a ranar 7 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.