Zan kafa cibiyar tunawa da Shagari - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wajen ta'aziyar Marigayi Shehu Shagari

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Marigayi Shagari ya kasance a tsare a tsawon mulkin soji na Buhari na watanni 20

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatinsa za ta kafa wata cibiya domin tunawa da Tsohon shugaban farar hula na farko a kasar Alhaji Shehu Shagari.

Buhari ya fadi hakan ne ranar Lahadi lokacin da yake ta'aziyya ga iyalai da gwamnati da kuma al'ummar jiharsa ta Sakkwato a gidan marigayin da ke birnin Sakkwato.Marigayi Shehu Shagari ya rasu ranar Juma'a a babban birnin kasar Abuja yana da shekaru 93."Gwamnatin tarayya za ta kafa wata cibiya domin tunawa da Marigayi tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari wadda za ta dace da matsayi irin nasa;" a cewar wasikar ta'aziyya ta shugaban kasar."

Gwamnan jihar ta Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne ya karanto wasikar ga taron masu zaman makoki yayin da shugaban kasar ke zaune cikin wani yanayi na juyayi.

Shugaban ya ce ya kadu da samun labarin rasuwar fitaccen dan siyasar wadda ya bayyana babban abin alhinin ya game daukacin kasar."Marigayi Alhaji Shehu Shagari wani jigo ne na musamman kasancewar kusan shi ne jami'i na karshe da muke da shi a raye daga cikin wadanda suka kafa gwamnatin farko bayan samun 'yanci kai ta Sir Abubakar Tafawa Balewa kuma ga shi shugaban farar hulla na farko mai ikon zartarwa" in ji shi.Muhammadu Buhari ya kasance babban kwamanda a rundunar sojan kasar lokacin da Marigayi Shehu Shagari ya yi mulki tsakanin 1979 da 1983 kuma yana cikin sojojin da suka hambarar da gwamnatinsa wadda suka zarga da cin hanci da rashawa.Bayan juyin mulkin ne Buhari ya zamo shugaban mulkin soji, kuma Shagari ya kasance a tsare a tsawon mulkin Buhari na watanni 20 wanda ya fi mayar da hankali kan yaki da masu satar dukiyar kasar da kuma rashin da'a.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Buhari ya kai ziyarar ta'aziya ga iyalan Shagari