Jihar Sakkwato ta bayar da hutu don rasuwar Shagari

Gwamnan Sokoto tare da Buhari a wajen ta'aziyar Alhaji Shehu Shagari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Gwamnatin Jihar Sakkwato da ke arewacin Najeriya ta bayar da hutun kwana daya na ranar Litinin, domin jimami da kuma yin addu'oi ga marigayi tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari.

Sanarwar da kakakin gwamnan jihar Sakkwato Abubakar Shekara, ya fitar, ta yi kira ga dukkanin limaman masallatan jihar su sadaukar da ranar litinin domin yin addu'oi ga tsohon shugaban da kasa baki daya.

Sannan gwamnatin jihar ta bayar da umurnin sassauto da tutar kasar a gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu domin girmama marigayi Alhaji Shehu Shagari, shugaba na farko a Najeriya mai cikakken iko.

Marigayi Shehu Shagari ya rasu ranar Juma'a a babban birnin kasar Abuja yana da shekaru 93.

Buhari ya umurci a sassuto da tuta na kwana uku

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

An sassauta tuta a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin sassauta tutoci a fadin kasar daga ranar Lahadi.

Wata sanarwa da mai ba shugaban na Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar Buhari ya ce "marigayi Shagari ya kasance kusan mutum na karshe da ya yi alaka da gwamnatin farko ta Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, kuma shi ne shugaba na farko mai cikakken iko da aka zaba."

Shugaban ya kara da cewa a tsawon shekarun da suka yi musamman hulda a majalisar koli sun fahimci juna duk da bambancin da ke tsakaninsu a shekarun baya.

Muhammadu Buhari ne ya daure Shagari bayan kifar da gwamnatinsa a 1983.

Wane ne Shehu Shagari?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari

 • Dan asalin jihar Sakkwato ne a arewa maso yammacin Najeriya
 • An haife shi a shekarar 1925 a garin Shagari
 • Shi ne na shida ga maifinsa Aliyu
 • Dan siyasa ne Manomi kuma makiyayi
 • Malamin Makaranta ne marubucin wakoki da tarihi
 • Ya zama shugaban kasa ne karkashin jam'iyyar NPN
 • Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983
 • Bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa, Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a mulkin soja
 • Kafin Shagari ya zama shugaban kasa ya taba zama sakataren majalisar Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa
 • Ya rike mukaman minista daban-daban
 • Ya taba zama ministan ci gaban tattalin arziki a shekarar 1960
 • Ya taba zama ministan kula da harkokin cikin gida a shekarar I962
 • Ya taba rike ministan ayyuka da safiyo (1965).
 • Shagari ne Turakin Sakkwato, wanda babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Sarkin Musulmi.