Bidiyon yadda Buhari ya je ta’aziya gidan Shagari

Bidiyon yadda Buhari ya je ta’aziya gidan Shagari

Latsa alamar lasifika domin kallon bidiyon ziyarar Buhari a gidan Shagari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara Sokoto domin yin ta'aziya ga al'ummar jihar kan rasuwar tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari.

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne ya tarbi shugaba Buhari a filin saukar jirgin sama kafin ya nufi zuwa gidan marigayin inda ya yi wa iyalansa ta'aziya.

Marigayi Shehu Shagari ya rasu ranar Juma'a a babban birnin kasar Abuja yana da shekaru 93.

Karanta wasu karin labaran