Shagari ya bar wasiyar inda za a binne shi - Bala Shagari

Alhaji Bala Shagari
Bayanan hoto,

Babban Dan Alhaji Shehu Shagari, Kaftin Bala Shagari Sarkin garin Shagari

Tsohon shugaban Najeriya marigayi Alhaji Shehu Shagari shi ne ya nuna inda za a binne shi idan ya rasu a cewar iyalansa.

Babban dansa Alhaji Bala Shehu Shagari wanda shi ne Sarkin Shagari shi ne ya tabbatar wa da BBC da wasiyar da mahaifinsa ya bari.

Marigayi Shehu Shagari ya rasu ne a ranar Juma'a a babban birnin kasar Abuja yana da shekaru 93.

An binne shi ne kuma a wani kangon daki da ke wani sashen na gidansa da ke garin Shagari ranar Assabar.

Mutane da dama sun yi tsammanin za a rufe Turakin Sakkwaton ne a Hubbaren Shehu inda kabarin Sheikh Usmanu Danfodiyo da na yawancin sarakunan daular Usmaniyya suke.

Sarkin Shagari wanda ke amsa tambaya kan ko mahaifin nasa ya bar wata wasiyya, ya ce marigayin ya yi wannan wasiyyar ne fiye da shekaru 10 kafin rasuwarsa da yammacin ranar Juma'a.

"Mai alfarma Sarkin Musulmi ya taya mana cewa muna iya kai shi Hubbare amma sai na fada masa cewa shi ga inda ya ce a binne shi; kuma a Musulunce wasiya na gaba ga duk wani abu" in ji shi.

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayar da hutun kwana daya na ranar Litinin, domin jimami da kuma yin addu'oi ga marigayi tsohon shugaban na Najeriya Alhaji Shehu Shagari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuma ya bayar da umurnin sassauta tutoci a fadin kasar daga ranar Lahadi.