Sheikh Hasina ta sake lashe zaben firai ministar Bangladesh

Prime Minister Sheikh Hasina casts her vote in the morning during the general election in Dhaka, Bangladesh, December 30, 2018.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

PM Sheikh Hasina, who has been in power since 2009, casts her ballot on Sunday

Hukumar Zaben Bangladesh ta sanar da firai minisar Bangladesh Sheikh Hasina a matsayin wadda ta lashe zaben da aka yi a ranar Lahadi da gagarumin rinjaye a karo na uku.

Tun shekarar 2009 ta ke rike da madafin iko a Bangladesh.

Jam'iyyun adawa sun yi tir da abin da suka kira "zaben bogi", wanda aka sami tashin hankali da korafe-korafe na magudin zabe.

Jam'iyyar adawar ta sami kujeru bakwai ne kawai, kuma ta yi kira da a sake gudanar da wani zabe.

"Muna kira ga hukumar zabe da ta soke wannan zaben bogin nan take," inji Kamal Hossain wanda shi ne jagoran jam'iyyar adawa.

Ya kuma kara da cewa "Muna bukatar a sake gudanar da wannan zaben a karkashin wata gwamnatin rikon kwarya nan ba da jimawa ba".

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mata a kan layin kada kuri'a a birnin Dhaka na Bangladesh

Hukumar Zabe ta Bangladesh ta gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ta sami rahotanni "daga sassan kasar daban-daban" da ke cewa an tafka magudi, kuma ta ce za ta bincike lamarin.

Akalla mutum 17 sun rasa rayukansu a hargitsin da ya biyo bayan zaben tsakanin magoya bayan jam'iyya mai mulkin kasar da masu goyon bayan jam'iyyar adawa.

'Yan takara 47 sun janye daga tsayawa takara daf da a kammala kada kuri'a, bayan da suka yi zarhin an tafka magudi.

Ms Hasina ta fada wa BBC ranar Juma'a cewa "A bangare daya suna yin korafi. A daya bangaren kuma, suna sukar ma'aikatan jam'iyyarmu da shugabanninta. Wannan ne abin takaici da ke damun kasarmu".

Muhimmancin wannan zaben

Bangladesh kasar da Musulmai ke da rinjaye ne a cikin al'ummar da ta kai mutum miliyan 160.

Kasar ce ta farko da ta taimakawa dubban daruruwan 'yan kabilar Rohingya Musulmai bayan da suka tsere daga gallaza musun da ake yi a makwabciyar kasa ta Myanmar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani ya daba wa Salahuddin Ahmed wuka a wurin zabe a birnin Dhaka, shi ne da dan takara a karkashin jam'iyyar adawa ta BNP

An sami karuwar tashin hankali tsakanin magoya jam'iyyun da ke takara a kasar, kumamasu sukar lamirin gwamnati sun ce ba ta sauraren kukan al'ummar kasar bayan da ta shafe shekara 10 a kan mulki.

Su wane ne ke takara?

Akwai Khaleda Zia, wadda ke tsare a gidan yari bayan da aka same ta da laifin cin hanci da rashawa a farko wannan shekarar, kuma an hana tsayawa takara a wannan karon.

Tun da Khaleda Zia na tsare, sai jam'iyyarta ta tsayar da Kamal Hossain, wanda a baya ya taba rike mukamin minista a gwamnatin Sheikh Hasina. Shi ke jagorantar hadakar jam'iyyun siyasa mai suna Jatiya Oikya Front.

Amma Kamal Hussain, wanda ke da shekara 81 da haihuwa wanda kuma lauya ne bai tsaya takara a wannan zaben ba.

A shekarar 2014, jam'iyyar BNP ba ta tsaya takara ba, wannan na nufin zaben da aka yi na Lahadi shi ne karon farko da dukkan manyan jam'iyyun kasar suka tsayar da 'yan takara a cikin shekara 10 da ta gabata.