AIDS: 'Najeriya ba ta abin da ya dace'

SCIENCE PHOTO LIBRARY

Asalin hoton, Science Photo Library

Karancin magunguna da ma'aikatan lafiya masu kula da mutanen da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya, wani babban nakasu ne ga kokarin shawo kan cutar.

Wata kididdiga ta ce Najeriya ita ce kasa ta biyu da ta fi yawan masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki da mutane fiye da miliyan uku.

Wani babban jami'i mai yaki da cuta mai karya garkuwar jiki da ya yi aiki da Hukumar yaki da cutar AIDs ko SIDA ta Majalisar Dinkin Duniya, Malam Musa Bungudu ne ya bayyana haka a wata hira ta musamman da BBC.

A cewar jami'in, yankunan karkara ne aka fi fargaba kan yiwuwar kara samun bazuwar cutar da kuma karancin wayar da kai.

Ya ce: "Can akwai karancin fahimta na bukatar zuwa awon jini, kuma duk da yake addinai na ta fadakarwa game da haramcin zinace-zinace, amma duk da haka ana yin su. Yanzu ma luwadi ya shiga."

Malam Musa Bungudu ya ba da misalin cewa a jihar Sakkwato kadai, na da mutum 128, 000 amma bai wuce mutum 14, 000 ne suke kan magani ba.

Jami'in lafiyan ya ce sarakuna na da gagarumar rawar da za su taka wajen wayar da kai game da muhimmancin zuwa awon jini a tsakanin jama'a.

"A ce Sarkin Kano, shi da ke ba da ma sallar juma'a, a ce cikin masallacin ana gama salla, ana batun daura aure. Sai a ce to! Za a duba Sarki, ba wai don a ce yana da cutar, ko ba shi da ita ba. Don Allah dubi irin tasirin da hakan zai yi."

Ya ce a iyakar saninsa, gwamnatoci ba sa yin abin da ya dace daidai da bukatun da ake da su don yaki da cuta mai karya garkuwar jiki.

"Duk wanda ac cikin Najeriya yanzu, kila kana (shafe) kwana nawa ba ka ga an dauko wata magana ko ga rediyo ba, ko ga talbijin ko cikin masallaci ko cikin coci ko a kasuwa ko a wani wuri... Ba ka jin ana wata fadakarwa," in ji shi.

Ya bayyana damuwar cewa daga cikin mutum miliyan uku da dubu dari da ke da cutar bai wuce kashi talatin ba da ke kan magani. Saura ba sa kan magani, sun san ma suna da cutar?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Prep na cikin magungunan da masu fama da cutar HIV kan sha

Musa Bungudu ya ce kamata ya yi kowanne mutum mace ko namiji su tabbatar an gwada jininsu, musamman mata masu juna biyu don ganin ko suna da cutar ko ba su da ita.

Ya bukaci hukumomi su wadata asibitoci da kayan gwaji da magani, ta yadda za a iya bai wa mutane da zarar an gwada su.