Rasha ta kama Ba'amurke dan leken asiri a Moscow

Rasha na takin saka da kasashen yamma kan zargin leken asiri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rasha na takin saka da kasashen yamma kan zargin leken asiri

Hukumar hana leken asiri ta Rasha FSB ta bayyana cewa ta kama wani Ba'amurke dan leken asiri a Moscow.

Ta ce ta kama mutumin Paul Whelan ne a ranar 28 ga watan Disamba a babban birnin kasar, Moscow, inda aka gurfanar da shi a kan zargin ''leken asirin kasa."

Hukumar hana leken asirin ba ta yi wani karin bayani a kan batun ba.

Idan har Kotu ta kama shi da laifi, za yai iya kwashe shekara 10 zuwa 20 a gidan kaso, kamar yadda kafar yada labari ta Tass ta ruwaito.

Zargin leken asiri na cikin abubuwan da suka auku tsakanin alakar Rasha da Birtaniya da Amurka.

A farkon wannan watan ne, Amurka ta kama wata 'yar Rasha Maria Butina da zargin yi wa Rasha aiki, da yin kutse cikin kungiyoyin 'yan jam'iyyar Conservatives.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin

Haka zalika a watan Maris, Birtaniya da kasashen yamma sun kori ma'aikatan jakadancin Rasha sama da 100 bayan zargin kokarin kashe tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Skripal da diyarsa Yulia a Salisbury.

Rasha ta musanta zargin inda ita ma ta kori ma'aikatan jakadancin kasashen yamma da dama.