Wanda ya kirkiri Intanet ya mutu

Dr Roberts tare da abokansa wadanda suka kawo Imntanet Hakkin mallakar hoto CARLOS ALVAREZ
Image caption Dr Roberts tare da abokansa wadanda suka kawo Imntanet

Wani Ba'amurke, Larry Roberts mai kirkira-kirkire wanda ya taimaka aka kirkiri intanet ya mutu yana da shekara 81.

A 1960, ya kasance cikin wani bincike mai suna ARPA wanda aka kawo domin hada na'urori masu kwakwalwa su yi aiki a tare.

Kuma shi ne wanda ya dauki wasu injiniyoyin da suka hada sassa da kuma manhajar da ake bukata domin tsarin yayi aiki.

Tsarin Arpanet ne ya zama wani tubali da aka daura intanet da ake amfani da shi a yanzu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arpanet da zangon farko na fitar yanar gizo

Dr Roberts tare da Bob Kahn, Vint Cert da Len Kleinrock ne suka hada intanet.

Dr Roberts ya mutu ne a ranar 26 ga watan Disamba sakamakon bugun zuciya da ya same shi kamar yadda iyalinsa suka bayyana.

Labarai masu alaka