Mutum 20,000 aka kashe a Syria a 2018

Rikicin Syria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sama da mutum 500,000 aka kashe a syria

Kusan mutane dubu ashirin ne aka kashe a rikicin Syria a shekarar 2018 da ke karewa.

Kungiyar da ke sa ido a rikicin kasar ta Syrian Observatory for Humar Rights ta ce, wannan shi ne adadi mafi karanci tun da aka soma yakin basasar a shekaru takwas da suka wuce.

Cikin wadanda abin ya rutsa da su a 2018 har da fararen hula fiye da dubu shida da dari uku, da kuma kananan yara fiye da dubu daya da dari hudu.

Jimillar sama da mutum 500,000 aka kashe tun soma yakin na Syria a 2011.

Yakin na Syria ya haifar da kwarar 'yan gudun hijira da ba a taba gani ba tun yakin duniya.

Kungiyar ta ce shekarar 2014 ce mafi muni da aka fi kisan mutane, inda aka kashe mutum dubu saba'in da shida.

Rikicin Syria dai ya kara tsanancewa ne bayan bullar kungiyar IS da ke da'awar jihadi.

IS ta yi ikirarin kafa daular musulunci a Syria da Iraqi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Miliyoyin mutanen Syria ne suka koma 'yan gudun hijira