An kashe sojojin Najeriya da Nijar 10

Sojojin Najeriya biyar aka kashe a Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya biyar aka kashe a Nijar

An kashe sojoji akalla 10 a kan iyakar Nijar da Najeriya yayin wani farmaki na hadin guiwa kan 'yan fashi tsakanin dakurun kasashen biyu.

Sojojin Najeriya biyar da na Nijar biyar aka kashe kamar yadda ministan tsaron Nijar Kalla Mountari ya shaida wa kamfanin dillacin labaru na AFP.

Ya kuma ce an kashe 'yan bindiga 11 a farmakin da sojojin suka kaddamar a yankin Maradi kusa da kan iyaka da Najeriya.

Wasu rahotanni sun ce tun a ranar Asabar ne sojojin suka yi musayar wuta da 'yan bindigar a kan iyakar kasashen biyu, kuma sojoji da dama ne suka ji rauni.

Ana tunanin 'yan fashi ne masu satar mutane da shanu daga Zamfara suka tsallaka Nijar.

Nijar ta tura sojoji a watan Agusta a yankin da take iyaka da jihar Zamfara.

Hukumomin Nijar sun ce farmakin makwanni uku da sojojin kasar suka kaddamar tun a watan Satumba tare da hadin guiwa da na Najeriya ya taimaka an kashe 'yan fashi akalla 30.