'Muna cikin kunci duk da makwabtaka da Abuja'

Tashar jirgin kasa ta Abuja Hakkin mallakar hoto Presidency

Hausawa kan ce ganin kitse ake yi wa rogo. Wannan ne halin da za a iya kwatanta rayuwa a garuruwa irinsu Suleja da ke makwabtaka da babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Ta fuskar ababen more rayuwa, mazauna garin Suleja sun ce suna shan wahala don kuwa ba sa samun wutar lantarki yadda ya kamata, duk da gagarumar karuwar jama'ar da ake samu.

Ta fuskar lantarki, za ka ga galibin jama'ar garin na kashe makudan kudi wajen sayen mai don zuba wa na'urorin jannareto, in ji Mista Gabriel Uchenna wani mazaunin Suleja tsawon fiye da shekara talatin.

Ya ce a da, ba haka garin Suleja yake ba, amma a yanzu jama'a na ci gaba da karuwa matuka.

Shi ma Sulaiman Ahmed da ke yankin titin Moroko mai yawan hada-hada, ya ce a gaskiya suna fuskantar matsalar karancin ruwa.

A cewarsa: "Al'ummar yankin sun dogara ne kacokam ga wani famfon burtsatsai don samun ruwan sha. Da safe ma, za ka ga wasu mutanen ba sa samu, saboda an yi yawa."

Shugaban karamar hukumar Suleja, Honarabul Abdullahi Shu'aibu Maje ya ce yawancin kananan ma'aikata da ke kwadago a babban birnin tarayya, suna zaune da iyalinsu ne a garuruwa kamar Suleja.

"Da safe in ka tashi, in ka ga irin dubban jama'ar da ke fita daga Suleja zuwa aiki Abuja, haka ma da yamma (idan sun komo), Kuma duk jama'ar nan, 'ya'yansu da iyalansu a Suleja suke zama.

Suna zuwa makarantunmu na gwamnati a Suleja, suna zuwa asibitocinmu gabaki daya na gwamnati a Suleja," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ambaliyar ruwa na cikin matsalolin da Suleja ke fama da su

A shekarun baya, kamar shekara 20 da ta wuce, jama'ar da take Suleja, ba ta fi 200,000 zuwa 300,000 ba, amma yanzu sun wuce miliyan guda, in ji shugaban karamar hukumar.

Ba karamin cika ake a garin Suleja ba, musamman lokacin da El-Rufa'i yake ministan Abuja, inda aka tashi wasu kauyuka daga babban birnin a cewarsa, yawancinsu duk Suleja suka koma.

Wakilin BBC AbduSsalam Ahmed ya kuma leka babban asibitin Abuja, inda ya ce a can ana fama da cincirindon mutane da matsaloli iri daban-daban.

Wani magidanci da ya kai 'yarsa ganin likita, Yunusa Amadu ya ce ya ce 'yarsa ba ta da lafiya don haka ya kai ta asibiti, sai dai ya taras da cunkoson jama'a.

"Kai! Lamarin ba magana, saboda idan ka zo sai ka bata lokaci sosai, saboda yawan jama'a," in ji Malam Yunusa.

A cewarsa babban asibiti kamar na garin Suleja na bukatar karin ma'aikata ta yadda za su iya kula da dumbin jama'ar da kan je neman magani.

Hukumomin asibitin dai sun ki amincewa su yi karin haske ko martani game da kalubalan da ake fuskanta a cibiyar lafiya.