'Tsakiya na taimaka min wajen gane ranar al'adata'

Kungiyar na aiki da makarantu a yankunan Kamaru
Image caption Kungiyar na aiki da makarantu a yankunan Kamaru

A wani kauye a gefen garin Limbe, Manka mai shekara 15 ta ce, "duk lokacin da na tashi a aji sai a yi ta dariya, ban san dalili ba sai da wata daliba ta rada min a kunne cewa akwai jini a jikin kayan makaranta na."

"Sai na ji kamar kasa ta bude na fada domin raina ya bace. Wannan ya sa na yi kwanaki ban je makaranta ba sai da wata kawata ta karfafa min gwiwar komawa".

Kamar Manka, 'yan mata da yawa a Kamaru musamman a kauyuka ba sa iya kirga kwanakin al'adarsu kuma suna bata kayan jikinsu inda hakan kan janyo masu jin kunya.

Wata kungiya mai zaman kanta a Kamaru, mai suna Girls Excel, na koya wa 'yan mata yadda za su hada tsakiyar hannu da za ta rika tuna musu da ranakun al'adarsu.

Delphine Konda, shugabar kungiyar ta hori 'yan mata kan yadda za su shirya tsakiyar da duwatsu masu launi daban-daban.

Duwatsu masu launin ja su ne na lokacin al'ada, masu launin kore da masu launin ruwan hoda su ne na sauran kwanakin.

Image caption Duwatsun na taimaka masu wajen girga iya kwanakin al'adar 'yan mata

"Da taimakon likitoci da malaman jinya da muke aiki da su, suke shirya duwatsun," in ji Konda.

Ta kara da cewa a kauyuka, 'yan mata na kin zuwa makaranta saboda jini kan bata musu sutura, ba kamar a birane ba.

Akwai rukuni biyu na 'yan matan da muke koya wa, 'yan shekara 11 zuwa 15 kuma muna gaya musu cewa yana da alfanu su san yadda jikinsu ke aiki.

"Yanzu ina sa kunzuguna idan na kirga duwatsun tsakiyar.... kuma ina tsallake jin kunyar da na fuskanta a karon farko," Manka ta shaida wa BBC.

Image caption Duwatsu masu launin ja su ne na lokacin al'ada

Kungiyar ta horar da 'yan mata 2000 tare da samar da auduga a makarantu a yankunan arewa maso yammacin da kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Sai dai rikicin da ake yi a yankin da ke amfani da harshen Ingilishi ya sa, an rufe kungiyoyin makarantu.

Sai dai kungiyar mai zaman kanta na aiki da majami'u kuma tana fata za ta fara aiki da al'ummomin Musulmi a yankunan biyu.

Labarai masu alaka