Za mu yi amfani da na'urar Card Reader a 2019- INEC

An yi amfani da na'urar 'card reader' a zaben 2015 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi amfani da na'urar 'card reader' a zaben 2015

Hukumar zaben Najeriya wato INEC ta bayyana cewa za ta yi amfani da na'urar tantance sahihancin mazu zabe, wato Card Reader a zabukan da ake shirin yi a watannin Faburairu da Maris, kamar yadda aka yi a zabukan 2015.

Mai magana da yawun hukumar, Mallam Aliyu Bello ya ce ganin yadda na'urar ta taimaka wajen gudanar da sahihin zabe a shekarar 2015, ya sa a yanzu ma za a yi amfani da ita.

To amma hukumar ta ce ba za a yi amfani da na'urar ba wajen aikewa da sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi zuwa hedikwatarta dake Abuja - sai dai a kai sakamakon a takarda.

INEC ta yi wannan bayani ne makwanni bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da wata doka da majalisar dokokin kasar ta amince da ita wadda ta nemi a wajabta wa hukumar amfani da na'ura, a dukkan tsarin zabukan.

Mallam Aliyu Bello ya ce a cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi don ganin an yi sahihin zabe, ta kara inganta sauri da kuma nagartar na'urar yadda ba za a samu wata matsala ba.

Ana dai amfani da na'urar Card Reader ne wajen tantance katin zaben masu kada kuri'a.