Jirgin kasa ya yi hatsari a Legas

Lagos train accident Hakkin mallakar hoto LASSEMA

Hatsarin ya auku ne a unguwar Mangoro da ke unguwar Agegen jihar Legas in da ya raunata wasu mutane. Jirgin kasan mai tarago 17 ya taso ne daga unguwar Ilu ya bi ta Oshodi zuwa Ebute Metta, inda ya yi hatsarin da misalin karfe bakwai na safiyar yau kuma yana dauke ne da mutane da kayayyaki.

Kwamanda a hukumar kare hadurra ta kasa (FRSC), Emma Fekoyo ne ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa babu wanda ya mutu amma an samu raunuka.

Image caption Jirgin ya kaucewa hanyarsa ne

Wani wanda ya shaida afkuwar lamari, Ikechukwu Nwachuku ya bayyana cewa a daidai wani wuri da titin ya fashe a kan hanyar jirgin kasar ne jirgin ya kauce hanya ya kife.

Jami'an bada agaji na gaggawa da jami'an tsaro sun hallara a wurin inda suke taimakon wadanda suka samu rauni da kuma gyaran hanyar.

Fasinjojin jirgin sun fito inda suka karasa tafiyarsu a kasa saboda jirgin ya toshe hanyar wucewa.

Labarai masu alaka