An sace jakar Robert Mugabe mai dauke da naira miliyan 54

A shekarar 2017 ne aka hambare Mugabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A shekarar 2017 ne aka hambare Mugabe

An gurfanar da mutum uku a gaban kotun kasar Zimbabwe in da ake zarginsu da satar jakar tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe, wadda ke dauke da $150,000 (kimanin Naira Miliyan 54).

Wadanda ake zargin, sun kashe kudaden ne a kan sayen motoci, gidaje da kuma dabbobi.

'Yar uwar tsohon shugaban, Constantia Mugabe, na daga cikin wadanda ake zargin.

Ana zargin tana da makullan gidansa da ke a kauyen Zvimba a kusa da babban birnin kasar, Harare, in da ta bai wa sauran mutanen makullan.

Sauran wadanda ake zargin masu hidimomin gida ne a lokacin da aka yi satar wadda ta auku tsakanin 1 ga watan Disamba na 2018 zuwa Janairu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Emmerson Mnangagwa ne ya gaji Mugabe

Robert Mugabe ya jagoranci kasar na tsawon shekara 37, in da wasu ke zarginsa da kwashe kudaden kasar domin jin dadin kansa.

A shekarar 2017 ne sojojin kasar suka hambare Robert Mugabe mai shekara 94.

Labarai masu alaka