Trump ya yi barazanar sanya dokar ta-baci a Amurka

Trump a iyakar boda tsakanin Amurka da Mexico Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Trump a iyakar boda tsakanin Amurka da Mexico

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya jaddada barazanarsa ta kafa dokar ta-baci a Amurka domin ya samu kudin da za ya gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico.

Rashin jituwa tsakaninsa da 'yan Democrats ya sanya an dakatar da lamurran gwamnati na tsawon kwana 20 zuwa yanzu, hakan ya sanya ba a biya ma'aikatan gwamnatin tarayya 800,000 albashinsu ba.

A ranar Asabar, dakatar da ayyukan na gwamnati ya zama mafi tsawo a tarihin Amurka.

Trump ya bayyana cewa gina katangar, wani alkawari da ya dauka lokacin yakin neman zabe, abin da ake bukata domin magance matsalar tsaro sakamakon shigowar bakin haure.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yayin da ake nuna wa Trump abubuwan da aka amshe a boda

'Yan Democrats sun ce gina katangar "rashin 'da'a" ne kuma barnatar da kudaden jama'a ne.

Shugaban Amurkan ya ki amincewa ya sanya hannu domin a biya kudade kuma a dawo da ayyukan gwamnati - idan dai har ba a amince da $ 5.7bn na gina katangar ba.

Labarai masu alaka