Yadda aka yi wa mata dashen sabbin hannuwa

Corinne Hutton Hakkin mallakar hoto Find Your Feet
Image caption Corinne Hutton ta fuskanci matsaloli da dama kafin a yi tiyatar

An yi nasarar yi wa wata mata 'yar Scotland tiyata inda aka dasa mata sabbin hannuwa.

An dauki tsawon sa'a 12 ana yi wa Corinne hutton, 'yar Lochwinnoch, wacce ta rasa hannuwanta da kafafuwanta tiyata a asibitin leeds General Infirmary.

Matar ta rasa hannuwanta da kafafuwanta ne a shekarar 2013 bayan da tayi fama da cutar limoniya inda ta kusa rasa ranta.

A lokacin da take magana a kan gadonta na asibiti, Corinne ta godewa likitocin da suka kula da ita kuma ta ce: "Ina da hannuwa, kuma sun yi kama da nawa na asali."

"Yanzu ina da yatsu, kuma suna motsi. Farin cikina ba zai misaltu ba."

Masana sun dade suna neman hannuwan da za su dace ta matar wacce tsohuwar 'yar kasuwa ce, kuma wacce ta dade tana fafutukar wayar da kan al'umma kan dashen hannuwa da kafafuwa.

Hakkin mallakar hoto John Linton
Image caption Corinne Hutton tana wayar da kan al'umma ta hanyar zane jikinta

Cikin likitocin da suka yi mata aikin har da Farfesa Andrew Hart, wanda ya yi tiyatar cire mata hannuwa da kafafuwa a shekarar 2013 wanda kuma a yanzu ya zama abokinta.

Farfesa Simon Kay, wanda ya jagoranci tawagar likitocin, shi ne ya fara yin aikin dashen hannuwa a Birtaniya a 2016 kuma Corinne ita ce mutum ta shida da ya yi wa aiki.

Kafin ta rasa hannuwanta da kafafuwanta, Ms Hutton na da kamfanin zane-zane a birnin Glasgow.

Hakkin mallakar hoto Finding Your Feet
Image caption Corinne Hutton (a dama) ta taba hawa tsaunin Kilimanjaro

Labarai masu alaka