Gwamnatin Najeriya da MTN sun cimma matsaya

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya, NCC ta ci tarar MTN dala biyan 5 a shekarar 2015 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya, NCC ta ci tarar MTN dala biyan 5 a shekarar 2015

Gwamnatin Najeriya da kamfanin sadarwa na MTN sun cimma wata matsaya a wajen kotu kan takaddamar da su keyi kan fitar da wasu kudi da suka kai dalar amurka biliyan takwas daga kasar ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin kasar ta zargi kamfanin na kasar Afrika ta kudu ne da karya dokar hada-hadar kudaden ketare ta kasar.

Bangarorin biyu dai basu bayyana yadda suka cimma matsayar ba, amma ga dukkan alamu wannan dambarwa ta jefa tsoro a zukatan sauran masu zuba jari a kasar.

Gwamnatin ta bukaci kamfanin na MTN da ya dawo da dala biliyan 8 da miliyan 100 zuwa asusun babban bankin kasar na CBN, haka zalika ta bukaci kamfanin da ya biya wasu dala biliyan 2 na daban a matsayin kudin haraji.

Sai dai kamfanin na MTN yaki yarda da cewa ya fitar da kudin ba bisa ka'ida ba, kuma kan haka ne ya shigar da karar gwamnatin kasar kan tarar da aka nemi ya biya.

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya ce ta nemi ya biya tarar dala biyan 5 a shekarar 2015, saboda ta kasa toshe layikan abokan huldarta da basuyi rigista ba cikin wa'adin da aka bata.

Daga baya ne dai kuma hukumar ta rage kudin tarar zuwa dala biliyan daya da miliyan dari bakwai. A jiya Alhamis ne, babbar kotun tarayya dake Legas ta sanya yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a matsayin hukuncinta.

Hakan ya biyo bayan bayanin da lauyoyin MTN din suka yiwa alkalin da ke sauraren karar Saliu Sa'id cewa bangarorin biyu sun shawo kan takaddamar dake tsakaninsu.

Shima lauyan babban bankin kasar Harry Ukaejiofor ya tabbatar wa alkalin kotun cewa babu sauran sauraren kara a kotu, tare da neman kotun da ta sa yarjejeniyar cikin hukuncinta.

Labarai masu alaka