Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai I

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli bidiyon jana'izar marigayin a Lafiya

Al'umar jihar Nasarawa na ci gaba da juyayin rasuwar Sarki Alhaji Dr Isa Mustapha Agwai I wanda ya rasu ranar Alhamis a wani asibiti da ke Abuja Najeriya bayan ya yi fama da jinya.

Daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar basaraken, wacce aka gudanar a Fadar Sarkin Lafia.

Gwamnan jihar Alhaji Tanko Almakura, ya ce za a dade ana juyayin mutuwar basaraken da ya yi fice wajen hada kan al'uma da tabbatar da zaman lafiya tsakanin kabilu da mabiya addini daban-daban na jihar.

Almakura ya ce ''Sarki ya nuna halin dattako a tsahon rayuwarsa, wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyansa ta hanyar zama Uba ga jama'ar da ke karkashin ikonsa''.

An haifi marigayin ne a ranar 14 fa watan Augusta 1935.

An nada shi Sarkin Lafia a ranar 28 ga watan Mayu 1974.

Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura yayi ta'aziya ga iyalan mamacin da kuma masarautar Lafia da jama'ar Nasarawa.

Hakkin mallakar hoto @Dantatuu

Labarai masu alaka