Manyan Lauyoyi za su kare Alkalin alkalan Najeriya Onnoghen a kotu

Justice Walter Onnoghen Hakkin mallakar hoto National Judicial Council

Wasu manyan lauyoyi a Najeriya sun ce za su sadaukar da ayyukansu domin kare Alkalin alkalan kasar mai shari'a Walter Onnoghen a kotun da'ar ma'aikata.

A ranar litinin ne kotun da'ar ma'aikata ta ce Alkalin alkalan zai gurfana gabanta kan zargin kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman lokacin da kasar ke tunkarar babban zabe. Kamfanin dillacin labaru na Najeriya NAN ya ruwaito cewa cibiyar da ke bincike kan rashawa ARDI ita ce ta fara shigar da koken kan Alkalin Alkalan.

Bisa tsarin doka dole ne manyan ma'aikata da jami'an gwamnati su bayyana dukiyar da suka mallaka kafin karbar mukami da kuma bayan sun sauka a wani mataki na yaki da rashawa.

Mista Agbakoba ya shaida wa sashen turancin broka na BBC cewa hukumar NJC da ke sa ido kan al'amurran shari'a a Najeriya ce ya kamata ta dauki matakin.

Ya ce NJC da dukkanin alkalan Najeriya ke karkashinta ya kamata ta dauki matakin a kan Alkalin Alkalan.

Ya kara da cewa mai shari'a Onnoghen yana da rigar kariya kuma za a iya wanke shi.

Laifuka shida ake tuhumarsa, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

Hakkin mallakar hoto OAL.LAW
Image caption Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi na Najeriya Olisa Agbakoba

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin ya ce yana cikin wadanda za su kare Alkalin alkalan.

Ya kuma ce hanyoyi biyu kawai ake bi domin iya tsige Alkalin Alkalai da kundin tsarin mulki ya tanadar. Shi ne idan an gabatar da shi a 'yan majalisar dattawa kuma kashi biyu bisa uku sun jefa kuri'ar tsige shi.

Ko kuma Hukumar da ke kula da shari'a NJC ta tsige shi da kanta.

Labarai masu alaka