'City ba za ta sayi dan wasa ba a Janairu'

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Litinin ne Manchester City za ta kara da Wolverhampton Wanderers a karashen wasan mako na 22 a gasar Premier A Ettihad.

City tana ta biyu a kan teburin Premier da maki 50 da tazarar maki bakwai tsakaninta da Liverpool ta daya, wadda ta buga karawa ta 22 a ranar Asabar.

Liverpool ta yi nasarar cin Brighton daya mai ban haushi, kuma Mohamed Salah ne ya ci kwallon a bugun fenariti.

Pep Gaurdiola ya ce ba za su sayo dan kwallo ba a watan nan na Janairu, sai idan ta kama za su iya dauka aro na karamin lokaci.

Kocin ya kara da cewar a irin wannan lokacin ba za ka samu dan wasa mai kwari ba, domin kowacce kungiya ba ta son rabuwa da manyan 'yan kwallonta domin kakar wasa ta yi nisa.

Labarai masu alaka