Theresa May: Majalisar Birtaniya na iya tsige ta gobe

British PM Theresa May Hakkin mallakar hoto AFP

Lokaci na kurewa Firai ministar Birtaniya Theresa May a kokarin da ta ke yi na gamsar da 'yan majalisa domin su mara wa shirinta na ficewa daga Tarayyar Turai.

Saura kwana guda kafin majalisar ta kada kuri'a a kan batun.

Ana sa ran a yau Litinin za ta yi gargadi cewa majalisar na daf da hana kasar ficewa daga Tarayyar Turai idan babu wata yarjejeniyar yin hakan.

Ana sa rai Firai ministar za ta bayyana matsayarta game da batun, inda za ta ce rashin ficewa daga Tarayyar Turai zai yi wa kasa babbar illa.

Jam'iyyar adawa ta Labour ta lashi takobin gudanar da kuri'ar yanke kauna idan majalisar ta ki amincewa da matsayin na Misis May.

Jagoranta Jeremy Corbyn ya ce jam'iyyar ta Labour za ta juya wa yarjejeniyr ficewar baya kuma za ta fara shirin fuskantar zaben kasa baki daya idan batun ficewar bai sami karbuwa ba.

Ya fada wa BBC cewa jami'iyyarsa za ta nemi a kada kuri'a kan amincewa da jagorancin Misis May da zarar an yi watsi da yarjejeniyar.

Ana sa ran kimanin 'yan majalisa 100 daga jam'iyyar Conservative mai mulkin kasar da kuma guda 10 daga jam'iyyar DUP za su hade da 'yan jam'iyyar ta Labour domin kayar da kudurin Misis May na ficewa daga Tarayyar Turai.