'Yan bindiga sun kai hari a Nairobi

A member of the security forces Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaro sun yi wa ginin kawanya

An kai hari kan wani otal da ke birnin Nairobi na kasar Kenya.

An ji karar harbe-harben bindiga da fashewar wasu abubuwa a ginin da ke lardin Westlands, wanda otal din DusitD2 da wasu ofis-ofis ke ciki.

Kungiyar al-Shabab da ke da mazauni a Somalia ta dauki alhakin kai harin ko da yake ba ta yi karin bayani ba. Ganau sun hangi 'yan bidiga hudu sun shiga ginin.

Jama'a da ke cikin ginin sun yi ta fice wa daga cikinsa da rakiyar jami'an tsaro. An fitar da mutane da dama da suka yi jina-jina daga cikin ginin.

Image caption Vehicles were on fire in the car park and people are being evacuated

Mene ne sabon labari game da harin?

Wata mata da ke aiki a ginin da ke makwabtaka da wanda aka kai wa hari ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "Sai kawai na soma jin karar harbin bindiga, sannan na soma ganin mutane suna tserewa sun daga hannayensu sama yayin da wasu ke shiga wani banki domin su tsira."

An ji karar fashewar wasu abubuwa da kuma turnukewar hayaki, inda za ka ga motoci sun kama da wuta a wuraren ajiye su.

Wani dan sanda a wurin ya shaida wa wakilin BBC Ferdinand Omondi cewa: "Al'amura sun cabe. Mutane na mutuwa."

Babu cikakken bayani kan yawan mutanen da suka mutu ko wadanda suka jikkata.

Labarai masu alaka

Karin bayani