Yaki da cin hanci da rashawa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shin Buhari na samun nasara a yaki da cin hanci?

A Najeriya mafiya yawan 'yan kasar na auna nasara ko akasin hakan da aka samu wajen yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin kasar ke cewa tana yi da ayyukan hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC.

A don haka lokacin da shugaba Buhari ya karbi mulki, masu kada kuri'a da dama sun yi murna a lokacin da EFCC a karkashin jagorancin Ibrahim Mustapha Magu, ta fara tuhumar wasu manyan mutane da ake zargi da yin sama da fadi da dukiyar al'umma.

Mukaddashin kakakin hukumar, Tony Orilade ya bayyana irin nasarorin da ya ce hukumar ta samu, inda yace

"A cikin shekara uku hukumar EFCC ta samu kwato fiye da naira miliyan dubu dari bakwai na kudaden da aka sace, a bangaren hukunta mutane kuwa, hukumar ta samu nasara a shari'u fiye da dari bakwai."

To ko ya masana ke kallon wannan batu?

Farfesa Jibrin Ibrahim jami'i ne a cibiyar bunkasa dimokradiyya da ci gaban kasa ya ce

"A gaskiya shugaba Buhari ya yi kokari, tun da ya karbi mulki an kama mutane da dama ana bincikensu, an gurfanar da wasu da dama a gaban shari'a, wasu har an yanke musu hukuncin dauri. Sai dai nasarar da ya samu ba kamar yadda ake tsammani ba ne.''

Wasu daga cikin manyan dalilan da ke sanya shakku a zukatan jama'ar kasar kan sahihancin yaki da matsalar cin hanci da rashawa da gwamnati ke cewa tana yi sun hada da:

Jan kafar da wasu ke ganin gwamnatin na yi a wajen daukar mataki a kan zarge-zargen da ake yi wa wasu jami'an da ke da kusanci da fadar shugaban kasar da kuma daukar dogon lokaci a shari'un da ake yi wa wasu manyan mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Ga misali wasu 'yan kasar na ganin an dauki dogon lokaci kafin gwamnati ta dauki mataki a kan zargin da aka yi wa tsohon sakataren gwamnati, Babachir Lawal da tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri, Ambasada Ayodele Oke.

Haka kuma batun sake mayar da tsohon shugaban kwamitin asusun fansho, AbdurRasheed Maina bakin aiki tare da kara masa girma ya ja hankali sosai.

Hakazalika wasu daga cikin shari'u da aka dauki dogon lokaci ana yi sun hada da na tsohuwar ministar man kasar, Diezani Alison Madweke da tsohon mai ba da shawara kan harkar tsaro a gwamnatin da ta shude, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da tsohuwar ministar kudin kasar Nenadi Usman da tsohon shugaban katafaren kamfanin mai na kasar NNPC, Andrew Yakubu,

baya ga tsofaffin gwamnoni da manyan 'yan siyasa.

To ko me ya sa hukumar ta gaza samun nasara a hakunci a kan irin wadannan shari'u? Mista Orilade ya bayyana cewa,

"EFCC hukuma ce da kawai ta ke iya gabatar da tuhuma, kuma dole sai bangaren shari'a ta taka nata rawar kafin a samu hukunta wadanda ake zargi, mu dai muna iya bakin kokarinmu."

Ya kuma kara da cewa "hukunta wadannan manyan mutane ba abu ne mai sauki ba domin kowannensu yana da tawagar kwararrun lauyoyi da ke kare shi, sannan sai su yi ta daukaka kara a kan abin da bai taka kara ya karya ba, don kawai suna da makudan kudaden da za su iya kashewa."

Amma Mista Orilade ya musanta zargin da wasu suke yi wa hukumar na farautar 'yan adawa, inda ya ba da misali da cewa an daure tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Chibi Dariye wanda a halin yanzu yake kurkuku kuma dan jam'iyyar APC mai mulki ne.

Sai dai wani zargin cin hancin wanda a baya-bayan nan ya yi matukar jan hankali a ciki da wajen kasar, shi ne na wani bidiyon da aka yi ta yadawa, wanda ake zargin gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da karbar na goro, batun da hukumar ta EFCC ta ki cewa komai a kai.

Mista Orilade dai ya bayyana cewa "shugaban hukumar mu ya ce ba za mu ce komai game da wannan batu ga jama'a ba, saboda batu ne da ke gaban kotu, amma hakan ba yana nufin ba ma yin komai akai ba, sai dai ba za mu fito mu bayyana abin da muke yi a kafafen yada labarai ba."

Wannan batu dai ya jawo cece-kuce mai zafi, inda wasu ke kira ga gwamnan ya yi murabus, yayin da wasu kuma ke ganin yana da kariya da kundin tsarin mulki ya bashi.

Wasu masu sharhi dai na ganin sai gwamnati ta tashi tsaye wajen yaki da cin hanci da rashawa hatta a bangaren shari'a kafin ta cimma gagarumar nasarar da 'yan kasar da dama ke fatan a samu a yaki da cin hanci da rashawa, matsalar da ke janyo koma baya a fannoni daban-daban na ci gaban kasa, musamman ta fannin tattalin arziki.