Ana hana 'yan gudun hijirar Najeriya shiga Kamaru - Amnesty

'Yan gudun hijirar Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daruruwan 'yan gudun hijira ne suka tsere daga Rann

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce Kamaru na taso keyar 'yan Najeriya da ke gudun hijira zuwa kasar saboda Boko Haram.

Kakakin kungiyar ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaron Kamaru ne ke dawo da 'yan Najeriya da suka tsallaka kasar domin gujewa hare-haren Boko Haram.

Wannan na zuwa ne bayan Amnesty ta wallafa wasu hotuna a shafinta na intanet na taurarorin dan adam kan girman barnar da mayakan Boko Haram suka yi a harin da suka kai garin Rann da ke jihar Borno a ranar litinin.

Rundunar sojojin Najeriya ta sha sukar kungiyar Amnesty inda a watan Disamba ta zargi kungiyar da kokarin yin zagon kasa ga nasarori da kuma yakin da take da Boko Haram.

Amnesty ta ce daruruwan mutane ne suka tsallaka iyakar Najeriya zuwa Kamaru daga garin Rann.

Kungiyar ta nuna hotuna da ta ce sama da gidaje 100 ne Boko Haram ta kone a garin na Rann tare da yin Allah wadai da harin.

Hakkin mallakar hoto Amnesty

Ta kuma ce wannan ya tabbatar da rahoton farko na kungiyar likitoci M├ędecin sans Frontieres game da halin da garin yake ciki.

Garin Rann da ke kunshe da sansanonin 'yan gudun hijira dama, ya sha fama da hare-haren Boko Haram a 'yan watannin nan.

Labarai masu alaka