Muhawarar jihar Kano: Tasirin Rimi a siyasar Kano #BBCNigeria2019

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Rimi na jam'iyyar PRP ne farar hular da ya fara mulkin jihar
  • Ana sabunta wannan shafin musamman don muhawarar jihar Kano ne daga lokaci zuwa lokaci.

Daga Maude Rabi'u Gwadabe, mawallafin jaridar shafin intanet, Kano Today

Muhammadu Abubakar Rimi shi ne zababben gwamnan jihar Kano na farko. A kansa Kanawa suka fara ganin gwamnan farar hula don haka ya zama mizanin da ake amfani da shi wurin auna dukkan gwamnonin da suka biyo bayansa.

Tasirin Rimi a siyasar Kano ya shafi yadda ake gudanar da gwamnati, da yadda ake tsara harkokin siyasa da kuma dangantakar gwamna da al'ummar da suka zabe shi.

Tarihi

An haifi Muhammadu Abubakar Rimi a shekarar 1940 a garin Rimi da ke karamar hukumar Sumaila.

Ya yi karatun boko har zuwa matakin digiri na biyu akan hulda da kasashen waje.

Ya kammala wannan karatun ne a 1975 a jami'ar Sussex da ke Ingila.

Ya yi aikin malanta a Zaria da Sokoto.

Ya kuma yi aiki a ofishin jakadancin Nigeria da ke Masar da kuma cibiyar nazarin hulda da kasashen waje ta Nigeria da ke Legas.

A 1977 an zabi Rimi a matsayin dan majalisar shirya kundin tsarin mulkin Nigeria inda ya wakilci Gwarzo da Karaye.

Da shi aka kafa jam'iyyar PRP a Disamban 1978.

Rimi Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Rimi ya yi ministan sadarwa a zamanin Abacha

Ya zama gwamnan Kano na farko daga 1979 zuwa 1983 a tutar jam'iyyar PRP.

Sai dai bambancin ra'ayin siyasa tsakaninsa da jagoran PRP Malam Aminu Kano ya sa Rimi ficewa tare da kafa jam'iyyar PPP.

Jam'iyyar PPP ba ta samu rajista ba, hakan ya tilastawa Rimi da mabiyansa 'yan santsi shiga jam'iyyar NPP.

Ya ajiye mulkin Kano a 1983 inda ya shiga takara karkashin NPP, amma bai yi nasara ba.

Bayan juyin mulkin soja, ya na daga cikin 'yan siyasar da gwamnatin Manjo Janar Buhari ta daure tsawon shekaru daruruwa.

A lokacin mulkin Janar Babangida, Rimi ya shiga jam'iyyar SDP kuma ya taka rawa wurin assasa a jihohin Kano da Jigawa.

A zaben gwamnoni na 1991, Abubakar Rimi ya bukaci magoya bayansa da su zabi dan takarar jam'iyyar adawa ta NRC, abinda ya bai wa Kabiru Gaya damar darewa mulkin jihar Kano.

Bayan juyin mulkin Janar Abacha a 1993, an nada Abubakar Rimi ministan sadarwa.

Amma daga karshen mulkin Abacha, Rimi na daga cikin 'yan siyasa 18 da suka rubuuta wa gwamnati wasikar bijirewa tare da neman mika mulki ga farar hula.

Wannan hadakar 'yan siyasa ta G-18 ita ce ta rikide zuwa G-34 sannan ta zamo jam'iyyar PDP wacce ta mulki Najeriya bayan mayar da mulki ga farar hula.

Ya nemi takarar shugaban kasa a 1999 da 2003 a jam'iyyar PDP amma bai yi nasara ba a zaben cikin gida.

Rimi ya sauya sheka daga PDP zuwa AC kafin daga bisani ya sake komawa PDP.

A shekarar 2006 aka yi wa matarsa Hajiya Sa'adatu kisan-gilla.

Ya rasu ranar 4 ga Afrilu 2010, inda ya bar mata daya da 'ya'ya takwas.

Limamin Chanji

A zamanin da ya ke gwamnan Kano, marigayi Abubakar Rimi ya kawo sauye-sauye da dama a gudanar da mulki da kuma ceton talakawa.

Hakan ya sa ake masa lakabi da Limamin Chanji.

A ranar da aka rantsar da shi ya soke Jangali da Haraji. Wannan ya ceto makiyaya da talakawa musamman a yankunan karkara daga zaluncin da suke fuskanta daga dagatai da masu unguwanni.

Sai dai hakan ya sa mutanen jihar Kano har kawo yanzu na kyashin biyan haraji.

Abubakar Rimi ya dauko 'yan boko ya nada su mukaman kwamishinoni, inda baki daya kwamishinonin zamaninsa suna da matakin karatu na digiri.

Shi ne ya fara bada hutun ranar ma'aikata wanda daga bisani gwamnantin Tarayyar Najeriya ta kwaikwaya.

Ya kafa hukumar yaki da jahilci, da Hukumar Ilmin Firamare, da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a yankunan karkara da kuma Hukumar Kula da Muhalli da Tsarin Birane.

Wadannan hukumomi sun bai wa gwamanati damar samar da aikace-aikace na Zahiri kamar tituna, makarantu, da asibitoci.

Kawo yanzu duk wanda ya yi gwamna a Kano na kokarin ya samar da ayyuka na zahiri a kokarin koyi da gwamnatin Rimi.

Gwamnatinsa ta bullo da shirin bai wa daliban sakandare alawus na wata-wata tare da tura dalibai zuwa kasashen waje domin yin karatun digiri.

A yanzu haka mafi yawan manyan likitoci da jami'an kiwon lafiya na jihar Kano mutane ne da su ka ci gajiyar wannan shiri.

Ya kafa gidan talabijin na CTV (ARTV a yanzu) da kamfanin wallafa jaridun Triumph. Wadannan kafafen yada labarai sun taimaka wurin yada manufofin gwamnatinsa da kuma yakar jam'iyyar NPN mai mulkin kasa a wannan lokaci.

Samuwar wadannan kafafen yada labarai ya bada damar horar da kwararrun 'yan jarida da dama a fadin Nigeria.

Haka kuma wadannan kafafen yada labarai sun ginu ne bisa akida ta siyasa, abinda ya sa ake masu kallon 'yan-amshin-Shata masu mika wuya ga dukkan gwamnatin da ludayinta ke kan dawo.

A yunkurin Rimi na kawo sauyi, bai nuna shayin kowa ba balle tsoro. Ya ja da sarakai, ya buga da masu kudi, kuma ya kara da malamai.

A zamanin da yake gwamna, Rimi ya dakatar da taba, ya soke Hawan Sallah a Kano, ya dakatar da sarkin Kano tsawon watanni shida, sannan ya nada sarkin Kazaure ya rike shugabancin majalisar masarautar Kano.

Haka kuma ya kirkiro Karin masarautu hudu a jihar Kano da nufin karya karfin ikon masarautar Kano.

Uban kuturu ya yi kadan

Muhammadu Abubakar Rimi ya yi kaurin suna wurin tsageranci da kafiya kan ra'ayinsa ba tare da tausa harshe ba.

Mutum ne shi mai barkwanci da iya magana musaman abinda ya shafi shagube, gugar-zana da kuma cin mutuncin 'yan adawa.

A zamanin mulkinsa yana gabatar da wani shirin siyasa a Talabijin mai suna Lale Kati.

Irin kalaman da ya shahara da su sun hada da "Ko sama da kasa za su hadu, ko duniyar nan gatansa ne, da kuma Uban kuturuu ya yi kadan".

Wannan tsari shi ya haifar da irin shirye-shiryen siyasar da ake gabatarwa a wannan zamanin a gidajen rediyon jihar Kano.

Sannan kalaman da sojojin baka ke yi a wadannan shirye-shirye a iya cewa duk tasiri ne na marigayi Abubakar Rimi.

Haka ma zantuttukan manyan 'yan siyasa irinsu "mahaha" da "masu baki da kunu."

Aminu Kano Hakkin mallakar hoto Daily Trust

Hatta tsohon Uban gidansa, Malam Aminu Kano bai tsira daga bakinsa ba lokacin da sabanin siyasa ya shiga tsakaninsu.

A wani jawabi da Rimi ya gabatar zamanin siyasar Santsi da Tabo ya yi wa Aminu Kano shaguben "tsohon banza, ya tara mutanen banza, yana gaya masu zancen banza!"

Dan Sumaila kafi Naira kyawu

Tsagewar da jam'iyyar PRP ta yi, inda magoya bayan shugaban jam'iyya Aminu Kano suka kafe a Tabo yayin da magoya bayan gwamna Rimi Santsi ya kwashe su ta tilastawa Abubakar Rimi sauya salon tsarin siyasarsa.

Ya ci gaba da gwagwarmayar kawo canji, inda ya yi kokarin dasa soyyarsa cikin zukatan jama'a ta yadda za su bi shi duk jam'iyyar da ya koma.

Gwamna Rimi ya ja hankalin Kanawa zuwa ga kyawun halittar da Allah ya ba shi, hakan ta sa har ake masa kirari "Dan Sumaila kafi Naira kyawu."

Shi da kansa yakan ce mata suna ado da hotonsa a dakunansu ko da kuwa 'yan akidar Tabo ne ko NPN.

Bayan haka ya gina tsarin gidan siyasa na biyayya ga Ubangida duk da cewa shi ya yi wa nasa tawaye.

Tasirin wannan ya kawo har wannan jamhuriya ta hudu da muke ciki.

Lokacin da aka kafa jam'iyyar PDP a jihar Kano, Rimi da abokan burminsa sun kwatanta jam'iyyar da murhu mai duwatsu uku; Santsi, Tabo, da NPN.

Wanann ta tilasta wa matasan da ba su yi siyasar jamhuriya ta biyu ba yin mubaya'a ga daya daga cikin wadannan gidaje uku domin samun damar dama da su.

Wannan dabi'a ta gida-gida tana ci gaba da tasiri a siyasar Kano, inda yanzu haka ake fama da Gandujiyya, Kwankwasiyya, Shekariyya da dai sauransu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Za a yi muhawarar ne a ranar Asabar

Kano ta yi gwamnoni 18 a tsawon shekara 52

A ranar Asabar ne BBC za ta kawo maku muhawarar 'yan takarar gwamna a jihar Kano.

Kwamishinan 'yan sanda Audu Bako ne ya fara mulkar jihar tsakanin watan Mayun shekarar 1967 zuwa watan Yulin shekarar 1975.

Audu Bako Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Kwamishinan 'yan sanda Audu Bako ne ya fara zama gwamnan jihar Kano

Sai gwamnan mulkin soja Kanar Sani Bello wanda ya shugabancin jihar tsakanin watan Yulin 1975 zuwa watan Satumbar 1978.

Daga nan ne sai Group Captain Ishaya Shekari wanda ya mulki jihar har zuwa watan Oktoban shekarar 1979.

Rimi Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Rimi na jam'iyyar PRP ne farar hular da ya fara mulkin jihar

Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi na jam'iyyar PRP shi ne farar hular da ya fara mulkin jihar a watan Oktoban shekarar 1979 har zuwa watan Mayun shekarar 1983.

Daga nan ne sai Alhaji Abdu Dawakin Tofa na jam'iyyar PRP ya fara shugabancin jihar har zuwa watan Oktoban shekarar 1983.

Sai Alhaji Sabo Bakin Zuwo shi ma dan jam'iyyar PRP ne kuma ya yi gwamna har zuwa watan Disambar 1983.

Bayan hambarar da gwamnatin Shugaban Najeriya Shehu Shagari, sai sojoji suka kara dawowa mulkin jihar.

Air Commodore Hamza Abdullahi ya mulki daga watan Janairun 1984 zuwa watan Agustan 1985.

Kanar Ahmed Muhammad Daku daga watan Agustan 1985 zuwa shekarar 1987.

Daga nan sai Group Captain Mohammed Ndatsu Umaru daga watan Disambar 1987 zuwa watan Yulin shekarar 1988.

Sai Kanar Idris Garba wanda ya yi gwamna tsakanin watan Agustan 1988 zuwa Janairun 1992.

Daga nan sai mulkin jihar ya koma hannun farar hula, inda Kabiru Ibrahim Gaya na jam'iyyar NRC wanda ya kasance gwamna tsakanin watan Janairun 1992 zuwa Novamban 1993.

Mulkin jihar ya kara komawa hannun soji, inda Kanar Muhammadu Abdullahi Wase ya yi gwamna tsakanin watan Disamban 1993 zuwa Yunin 1996.

Sai Kanar Dominic Oneya wanda ya yi gwamna tsakanin watan Agustan 1996 zuwa Satumbar 1998.

Daga nan ne sai Kanar Aminu Isa Kontagora wanda ya shugabancin jihar tsakanin watan Satumbar 1998 zuwa watan Mayun shekarar 1999.

Bayan da Najeriya ta koma mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, mulki ya kara koma wa hannun fararen hula.

Rabiu Musa Kwankwaso
Image caption Sau biyu Kwankwaso ya yi gwamnan jihar Kano

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar PDP ya yi gwamna tsakanin watan Mayun shekarar 1999 zuwa watan Mayun 2003.

Sai Malam Ibrahim Shekarau na jam'iyyar ANPP wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2011.

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya sake dawo kujerar gwamna tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto Kano government
Image caption Ganduje yana neman wa'adi na biyu

A karshe, sai gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC wanda ya fara mulki daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Tasirin Malam Aminu a siyasar Jihar Kano #BBCNigeria2019

Daga Mahmud Jega, mataimakin babban edita a jaridar Daily Trust

Ko a lokacin da Malam Aminu Kano yake Malamin makaranta shekarun 1940, an san shi da zafi kuma ba ya barin ko ta kwana.

Marigayi Sheik Abubakar Gumi ya ba da wani labari a cikin littafinsa a kan wani abu da ya faru tsakaninsa da Aminu Kano a lokacin da suke aikin karantarwa a makarantar horar da Malamai ta Maru a shekarun 1940.

Labari ne a kan limamin masallaci wanda yake taimama kafin ya ja sallah, haka dai aka samu Malam Aminu ya yi kokari wajen sauya ra'ayin limamin a kan yin hakan.

Ba abin mamaki ba ne a kan mutum mai kwarjini irin Aminu Kano wanda yake da fada a ji a bangarorin ilimin Islama da na Boko, ya zama jajirtacen dan siyasa da ya yi fice a Kano da Najeriya ma baki daya.

Bayan Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello, ba na tunanin akwai wani dan siyasa da ya ba da gudunmawa wajen ci gaban siyasa da al'umma a arewacin Najeriya kamar Malam Aminu Kano.

Tasirinsa

Tasirinsa ya yi karfi a mahifarsa Kano inda aka kafa jam'iyyarsa ta farko a 1950 mai suna Northern Elements Progressive Union (NEPU).

Ba kamar siyasar da ba, siyasar yanzu ba a yinta bisa akida, NEPU tana da bambancin akida sosai da abokiyar hamayyarta wacce ita ce jam'iyyar Sardauna mai suna Northern Peoples Congress (NPC).

Kofar dan agundi Hakkin mallakar hoto Getty Images

A wannan lokaci NEPU tana kira ne ga ra'ayin gurguzu inda ta kira tsarin NPC da zaluncin sarakunan gargajiya da na N.A, haka ma suna adawa da mulkin mallaka na Turawan Ingila, inda suke kan gaba wajen kwato hakkin talakawa.

A 1978, Malam Aminu Kano ya kirkiri sabuwar jam'iyya mai suna Peoples Redemption Party (PRP) wadda ta fi NEPU tasiri saboda PRP ta kawo kujerar gwamna a Kaduna da Kano a 1979 da kuma kashi uku cikin hudu na 'yan majalisar jiha a Kano.

A wasu sassan arewacin Najeriya, PRP ba ta yi tasiri sosai ba, Malam Aminu ya yi takarar shugaban kasa a 1979 inda Shehu Shagari ya samu nasara.

A 1981, PRP ta rabu biyu, bangaren Tabo wanda Malam Aminu yake jagoranta sai kuma bangaren Santsi wanda Chief Michael Imoudu ya jagoranta tare da Gwamnan Kano Abubakar Rimi da na Kaduna Balarabe Musa a wancan lokaci.

Wannan rabuwar kan ta kawo matsala sosai ga PRP.

Malam Aminu Kano ya rasu kafin zaben 1983 inda Khalifa Hassan Yusuf ya maye gurbinsa a matsayin shugaban PRP wanda ya rasu a watan Janairun 2019.

Ko bayan mutuwar Malam Aminu Kano, PRP sai da ta lashe zaben gwamna a Kano a zaben 1983 amma ba ta samu nasara a Kaduna ba.

Har yanzu akwai jam'iyyar PRP kuma tana bisa akidu irin na Aminu Kano.

Malam Aminu dai ya kafa tarihi a siyasa ba wai a Kano ba kawai, amma a Najeriya baki daya.

Wannan layi ne
mata gwamna a kano

A yayin da zaben 2019 ke tunkarowa, an samu mata guda bakwai da ke takarar gwamnan jihar Kano.

Sai dai inda gizo ke saka shi ne, anya Kanawa za su iya zabar mace a matsayin gwamna?

Jihar Kano ita ce jiha mafi yawan al'umma a Najeriya kuma ana daukarta a matsayin cibiyar siyasar arewacin Nigeria.

Kano ta yi fice a kan siyasar gwagwarmaya da neman kawo sauyi tun daga jamhuriya ta farko.

Sai dai kuma duk da wannan jagaban da Kano ke yi a al'amuran siyasa musamman a arewacin Nigeria, kawo yanzu ba a taba samun mace ta zama gwamna ba.

Addini da Al'ada

Mafi rinjayen al'ummar Kano Musulmi ne. Haka kuma ana iya cewa daukacin 'yan asalin jihar Kano Hausawa ne ko da yake da yawansu na da jinin Fulani, Kanuri, Bugaje kai har ma da Larabawa.

Don haka ana iya alakanta rashin samun gwamna mace da tasirin addinin Islama da kuma al'adun Hausawa.

A bisa fahimtar addinin Musulunci wadda ta fi rinjaye a tsakanin al'ummar Kano, haramun ne mace ta shugabanci al'umma.

Ko da yake wasu malaman na ganin cewa mata za su iya wakilci amma ban da shugabanci dungurungum.

Haka kuma a al'adance, mata ba sa shugabanci.

Hausawa kan dauka cewa duk gidan da mace ke shugabanta ya lalace, balle kuma a yi batun jiha baki daya.

Sauyin Zamani

Duk da tasirin addini da al'ada a cikin rayuwar al'ummar Kano, sauyin zamani ya sa abubuwan da a baya kan zama bambarakwai yanzu sun zama gama-gari.

A yanzu haka kusan duk ayyukan da maza ke yi in ban da aikin karfi mata ma na yi.

Tasirin karatun boko ya sa mata da dama na rike shugabanci a hukumomi da yawa.

Tun zamanin jamhuriya ta biyu ake mata kwamishinoni a Kano, inda maza ke aiki a karkashinsu ba tare da samun matsala ba.

Dubban mata na shugabantar makarantun boko tun daga firamare zuwa sakandire da manyan karatun ilimi mai zurfi.

Ta bangaren addini ma ana samun karuwar ilimi da fatawoyi da ke nuna halarcin shugabancin mata.

Mata a siyasa

A fagen siyasa, an samu fitattun mata uku da suka ci zaben majalisun dokokin tarayyar Najeriya daga jihar Kano.

Marigayiya Kande Balarabe ta wakilci mazabar Dawakin Tofa a majalisar tarayyar a zamanin jamhuriya ta biyu karkashin tutar jam'iyyar PRP.

A zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha, an zabi Naja'atu Bala Muhammad a matsayin 'yar majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya karkashin jam'iyyar DPN.

Sai dai kuma kafin rantsar da su Allah ya karbi ran Abacha.

A cikin jamhuriya ta hudu Azumi Namadi Bebeji ta wakilci mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai ta tarayya a tutar jam'iyyar ANPP.

Wannan na nuna alamar cewa mata na iya cin zaben siyasa a Kano.

Kalubalenku mata

A fahimtata, wayewar siyasar Kanawa ta kai yadda za su iya zabar mace gwamna.

Amma fa babu yadda za a yi a zabi mace gwamna har sai an samu macen da ke yin abin da maza ke yi su zama gwamna.

Baki daya matan da ke takarar gwamnan Kano a zaben bana sun fito ne a kananan jam'iyyu marasa tasiri.

Idan har mata na son zama gwamna a kano sai sun shiga jam'iyyu masu rinjaye su fafata da takwarorinsu maza wurin karbar iko a jam'iyyun.

Wannan ba abu ne mai sauki ba amma idan aka samu macen da ta zage, ta kai wannan matsayin babu dalilin da zai sa Kanawa kin zabenta.

Ranar 22 ga watan Janairun 2019

Kano ta Dabo tumbin giwa, tunjumin gari mai Dala da Gwauron Dutse, gari ba Kano ba dajin Allah! Wannan shi ne kirarin da aka jima ana yi wannan birni ko in ce jiha, wadda za a iya cewa kusan ita ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.

A yanzu dai a iya cewa kwanaki ne suka rage kafin ranar da za a yi zabukan Najeriya da suka hada da na gwamnoni a jihohin kasar, ciki kuwa har da Kano.

Haka kuma, a nan BBC muka zage wajen shirya muhawara ta 'yan takarar gwamna a wasu jihohin kasar da suka hada da Kanon, kuma aski ya zo gaban goshi, domin kuwa ranar 31 ga watan Janairun nan ne za a tafka ta tsakanin 'yan takara hudu maza da kuma mace daya.

Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Masu sharhi na ganin wannan muhawara tana iya sauya al'amura da dama, musamman sauya ra'ayin masu zabe kan wanda za su zaba, bayan sun ji shirin da kowane dan takara ke da shi.

A wannan makala dai, BBC ta yi nazari ne kan irin kalubalen da ke gaban duk wanda zai lashe zaben na 2019 na kujerar gwamnan Kano, da kuma nazari kan irin yadda zai iya tunkararsu.

A wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, mata da yawa sun fito takarar gwamna a jihar Kanon.

Jihar dai na daya daga cikin manyan jihohin arewacin Najeriya, kuma jiha ce wacce ta yi suna wajen tatagurzar siyasa.

A tarihin jihar dai mace ba ta taba rike wani mukami na shugabanci ba a matakin gwamna.

Matan bakwai sun fito ne a jam'iyyu daban-daban, kuma kowacce na da manufofinta na musamman ga al'ummar Kano idan ta lashe zaben.

Fauziyya Kabir Tukur ta zauna da hudu daga cikin wadannan matan ga kuma karin bayani a kansu.

Sannan kuma ta jiyo mana ta bakin wasu mazauna jihar kan ra'ayinsu kamar yadda za ku gani a bidiyon da ke sama.

Sai dai a irin hasashen da masana ke yi, suna ganin zai yi wuya mace 'yar takara ta kai labari a jiha irin Kano.

Tasirin muhawarar BBC a jihar Kano

Masu sharhi na ganin wannan muhawara tana iya sauya al'amura da dama, musamman sauya ra'ayin masu zabe kan wanda za su zaba, bayan sun ji shirin da kowane dan takara ke da shi.

A wannan makala dai, BBC ta yi nazari ne kan irin kalubalen da ke gaban duk wanda zai lashe zaben na 2019 na kujerar gwamnan Kano, da kuma nazari kan irin yadda zai iya tunkararsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Matsalolin Jihar Kano

Hakika duk wanda ya san jihar Kano to ya san babbar jiha ce da ba za ta rasa wasu manyan matsaloli da ke damunta ba, duk kuwa da irin ci gaban da ake samu da kuma sauye-sauye da wasu gwamnatoci na da da na yanzu suka samar mata.

Sai dai ba za mu mayar da hankali kan dukkansu ba, za mu zabi muhimmai ne daga cikinsu, wadanda muke ganin su ne manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta.

Cunkoson jama'a

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masana harkokin yau da kullum da dama a jihar Kano sun bayyana cewa cunkoson jama'a da kara tudadowar mutane cikin jihar na daga cikin manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta.

Malam Kabiru Sa'idu Sufi wani mai sharhi ne, kuma malami a makarantar share fagen shiga jami'a ta Kano, ya shaida wa BBC cewa: "Yawan jama'ar da ke kara shiga Kano ya sa abubuwan more rayuwa ba su wadata ba.

"Babu isassun tituna, babu isassun makarantu, ruwan sha, wutar lantarki duk ba su ishi yawan al'ummar jihar ba," in ji Malam Sufi.

Sai dai ya ci gaba da cewa: "Duk wanda zai zama gwamna yana bukatar bayar da kulawa ta musamman kuma ta gaggawa - don bukatar ta fi karfin abun da ke kasa a yanzu."

Bangaren ilimi

Malam Kabiru Sa'idu Sufi ya kara da cewa harkar ilimi a jihar Kaduna na ci gaba da tabarbarewa musamman a matakin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

"Yawan haihuwa da cunkoso a makarantun jihar musamman ganin hotunan da suka dinga yawo a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan, sun isa shaida wa mutum cewa harkar ilimi na cikin halin ha'u'la'i.

"Don haka duk wanda zai zamo gwamna na gaba na bukatar sanya dokar ta baci don shawo kan lamarin.

"Akwai bukatar kara yawan malamai, da ba su horo da kara yawan makarantu da samar da dukkan kayayyakin aiki a ake bukata," in ji Malam Sufi.

Lafiya uwar jiki

Rashin isassun asibitoci da wadatattun kayan aiki da isassu kuma kwararrun likitoci da ma'aikatan jinya na daga cikin manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta, kamar yadda Malam Sufi ya ce.

Ya kara da cewa: "Don haka ya zama wajibi ga gwamna mai zuwa ya dauki matakan da suka dace don kai wa gaci."

Yankunan karkara

Noma tushen arziki in ji masu magana, kuma kamar yadda aka sani mafi yawan manoma mazauna yankunan karkara ne, don haka akwai bukatar samar musu da filin noma da iri da taki da kuma dabarun noman zamani, in ji masanin.

Tattalin arziki

Kamar yadda aka sani ne tattalin arzikin Najeriya ba ma na Kano ba na fuskantar babban kalubale, don haka Malam Sufi ke ganin akwai bukatar bai wa dama su samu kudade a hannunsu.

"Babu kudo a hannun manoma da 'yan kasuwa, kuma hakan babban kalubale ne ga ci gaban tattalin arziki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

"Akwai bukatar samar musu da hanyoyin samun kudi a kuma samar wa mata jari a horar da su kan sana'o'i," a cewar masanin.

Yanzu dai abun da za a jira a gani shi ne, yadda gwamnan da zai lashe wannan zabe mai zuwa zai tunkari wadannan kalubale tare da warware su don ci gaban jihar Kano.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A da Kano na da arzikin gyada inda ake fitarwa wasu kasashen

Karin bayani