Zaben Najeriya: Wane dan takara Birtaniya da Amurka ke goyon baya?

Trump and May Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amurka da Birtaniya sun ce ba sa goyon bayan kowane dan takara daga cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaben da za a yi a watan Fabrairun bana.

Amurka ta ce tana sanya ido tare da sauran kasashe kan mutanen da ke katsalandan a harkokin siyasa, ko kuma suke rura wutar muzgunawa 'yan kasa gabanin zaben, ko da lokacin da ake yinsa ko bayan sa.

Burtaniya kuwa ta ce 'yan Najeriya ne kawai za su iya zabar wanda zai shugabance su, ta hanyar lumana da zabe na gaskiya.

Wata sanarwarar hadin gwiwa da ofisoshin jakadancin Amurka da Burntaniya a Najeriya suka fitar ta ce abinda kasashen biyu suke goyon baya shi ne tsarin dimokradiyya na gaskiya, da sahihin zabe da za a gudanar cikin zaman lafiya.

Amura ta ce za ta iya daukar matakai da suka hada da hana shiga Amurka kan duk mutumin da aka samu da hannu da rura wutar rikicin siyasa, ko kuma masu magudin zabe.

Sanarwar ta ce za kuma a iya daukar wannan mataki kan iyalan wanda aka samu da laifi.

Birtaniya ta ce za ta hada kai da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya wajen saka ido a zaben na Najeriya.

Sanarwar na zuwa ne kwana daya bayan wasu kafofin wasta labarai sun rawaito cewa Amurka na goyon bayan wani dan takara a zaben da za a yi na badi.