WhatsApp zai takaita tura sakonni don magance labaran bogi

WhatsApp shi ne kafar sadarwa wanda aka fi amfani da shi a duniya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption WhatsApp shi ne kafar sadarwa wanda aka fi amfani da shi a duniya.

Kamfanin WhatsApp zai rage damar tura sakonnin da ake tura wa mutane zuwa mutum biyar daga 20 da ake a halin yanzu.

WhatsApp ya bayyana cewa zai yi hakan ne a ci gaba da kokarin da yake na magance yada labaran bogi.

Kamfanin na WhatsApp wanda mallakin Facebook ne, ya kawo wannan tsarin a kasar Indiya watanni shida da suka gabata.

Wannan ya biyo bayan kisan da yada labaran bogi ya haifar ta hanyar amfani da shafin a kasar ta Indiya.

Image caption Facebook shi ne ke da manhajar WhatsApp

Kamfanin ya bayyana sabon tsarin ne a Jakarta da Indonesia.

Kamfanin ya shaida wa BBC cewa, ya dauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da ya yi .

Mai magana da yawun kamfanin na Whatsapp, ta ce za a rage yawan sakonnin da ake turawa ta kafar a fadin duniya.

Kamfanin ya ce yana fatan daukar wannan mataki zai taimaka matuka gaya wajen rage yada labaran bogi da ake yi ta hanyar amfani da kafar sadarwar, wanda hakan kuma ke janyo matsaloli da dama.

Karin bayani

A kwanakin baya ne kamfanin Facebook ya sanar da wasu sabbin matakai na rage yawan labarai na bogi da ake wallafawa a shafin sa.

Facebook dai ya yi ta shan suka akan yawan labarai na bogi da aka rika wallafawa a shafin sa gabannin zaben Amurka wanda ake zargin cewa, irin labaran da aka rika wallafawa sun taimaka kan yadda sakamakon zaben ya kasance.

Labaran bogi tamkar dan itaciyar tufa ne, zai iya kasancewa mai kyawun gani, amma idan ka gatse sai ka ji rubabbe ne sosai.

Tun bayan samuwar kafofin sada zumunta na zamani dai ana yawan samun matsala ta yada bayanan karya da kuma labaran kanzon-kurege sosai a kafofin.

Babbar matsalar kuma ita ce ta yadda mutane suka fi son samun bayanai daga kafofin sada zumuntar fiye da na kafafen yada labarai na ainihi.