Kun san Abu Bakar Ba'asyir, wanda ya kirkiri kungiyar masu tsaurin ra'ayi ta Ivy League?

Abu Bakar Ba'asyir a kotu a 2016. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anan zargin Abu Bakar Ba'asyir da karfafa kungiyoyin dake ikirarin jihadi wadanda suka kai harin Bali a 2002

Ana zarginsa da shirya kai harin Bali a 2002, da kuma kirkirar kungiyar "Ivy League School for Extremist" wato makarantar masu tsattsauran ra'ayi a Indonesia, inda yake kwaikwayon manyan jami'o'in Amurka.

Ya ci gaba da bayar da fatawowinsa har a cikin gidan yari, a 2014 kuma ya yi mubayi ga kungiyar IS.

Ya dauki mahukunta sama da shekara 10 suna kokarin kai shi gidan kaso a kan laifukan ta'addanci.

A wannan makon, Shugaba Joko Widodo ya dauki wani mataki mai rudani, inda ya ba da umarnin za a saki mutumin mai shekara 80 daga kurkuku saboda alfarma.

Masu tsaurin ra'ayi na kungiyar Ivy League

Malamin mabiyin Sunni ya jima yana jaddada bukatar tabbatar da shari'ar musulunci a Indonesia.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadansu daga cikin masu ikirarin jihadin da ke da hannu a harin Bali a 2002 sun halarci makarantar Ba'asyir

Ba'asyir ya yi suna ne a lokacin da ya kafa makarantar Al-Mukmin Islamic Boarding School, wadda ya kafa a tsakiyar birnin Java a 1972.

Jami'an gwamnatin Indonesia da sauran kungiyoyi sun bayyana cewa makarantar na koyar da tsattsauran ra'ayi da kuma yada kiyayya tsakanin dalibansa.

Mutane da yawa da suke da hannu a harin bam din na Bali wanda ya kashe mutane 200 a watan Oktoba na 2002, suna halartar makarantar Ba-asyir da koyarwarsa.

Ana nemansa saboda yi wa gwamnati zagon kasa

A 1982 ne aka yanke masa hukuncin zama gidan kaso saboda ayyukan da yake aikatawa na zagon kasa ga dokokin kasa inda ya nemi a kafa shari'ar musulunci a Indonesia, amma sai ya gudu ya bar kasar inda ya tafi Malaysia a 1985.

Sai bayan shekara 15 ya dawo inda ya taimaka aka assasa majalisar masu jihadi na kasar Indonesia "Indonesia Mujahidin Council (MMI).

Ana zargin Ba'asyir da kai hare-hare da dama a kan coci-coci a Indonesia a jajibirin ranar Kirismeti a shekarar 2000, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 18.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Jemaah Islamiyah kungiyar yan tada kayar baya ce mai alaka da Al Qaeda

Babban al'amarin ya auku ne a ranar 12 ga watan Oktoba na 2002, lokacin da wata mota mai dauke ta bam ta fashe a Bali, inda ya kashe mutane 202 - 88 'yan Australiya da 'yan Indonesia 38.

Ana zargin Ba'asyir ne shugaban addini na kungiyar Jemaah Islamiyah (JI), kungiyar addinin musulunci mai alaka da Al-Qaeda, wadda ta kai harin.

Kungiyar na da rajin kafa daular musulunci a Kudu maso Gabashin Asiya.

Laifin Ta'addanci

A shekaru da dama, mahukunta a Indonseia sun yi kokarin kai Ba'asir kurkuku a kan laifin ta'addanci.

A shekarar 2000, ya shiga kuma ya fita kurkuku, amma an kori laifuka masu alaka da tayar da bam a 2002 da 2003 saboda rashin kwararan hujjoji.

Ya zauna a gidan yari na wani lokaci kadan saboda sa hannunsa a harin bam na 2002 - wani hukunci wanda daga baya aka sauya.

A 2010, ma'aikata sun kai samame a hedikwatar Jemaah Ansharut Tauhid (JAT) - wata kungiya da Ba'asyir ya kafa a 2008.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An saki Ba'asyir daga kurkuku saboda rashin lafiya da kuma yawan shkeraunsa.

An zargi kungiyar da hadin gwiwa da sansanin horas da 'yan ta'adda a Aceh, wadda ke da manyan mambobin yan ta'adda na Indonesia.

Mahukunta sun ce babban burinsa shi ne na kai hari ga manyan jami'an gwamnati, domin ikirarin hada daular musulunci da yake.

An daure Ba'asyir a kan laifin ba su agaji da kudade da kuma taka rawa wajen kafa sansanin, inda aka daure shi a 2010.

Mubaya'a ga ISIS

Malamin ya musanta duka zargin da ake yi masa inda ya zargi Amurka da sa hannu wajen kokarin kai shi kurkuku.

Amma ya ci gaba da goyon bayan masu ikirarin jihadi yana cikin gidan yari.

A 2014, ya bayyana mubaya'arsa ga IS, a lokacin da ta mamaye wasu sassan Iraki da Syria.

An ruwaito cewa ya yi mubaya'ar ne tare da wasu mutane 23 a cikin dakin da suke sallah a gidan yarin Pasir Putih, inda yake a tsare.

Ko a gidan yari, Abu Bakar Ba'asyir, mutum ne mai tasiri wanda ke ci gaba da ba da fatawoyinsa daga gidan yari, wanda hakan ya ja hankalin mahukuntan kasar.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu tsokaci sun ce shugaba Widodo na kokarin nuna kishin addinin musulunci ne saboda zaben Afrillu.

Matakin Shugaban Widodo na sakin sa ya hadda rudani, mamaki da Allah wadai daga jama'a.

'Nesa da Gaskiya'

A wani rubutu da jaridar Jakarta Post ta fitar a ranar Litinin, jaridar ta ce "Gwamnati Widodo ta yi nesa daga gaskiya a kan bayanin dalilin sakin Ba'asyir."

Ba'asyir ya yi wa'adin da za a ba shi afuwa a watan Disamba, amma kin amincewarsa ya yi mubayi'a ga shugabannin kasar, daya daga cikin bukatun ba da alfarmar.

Amma sai ya hakikance cewa "Allah kawai zai bi."

Amma duk da hakan shugaban kasar Indonesia ya ba shi afuwa ba tare da wasu sharudda ba, inda aka zarge shi da yin hakan domin cimma burin siyasa.

Masu tsokaci sun bayyana cewa yana so ya yi amfani da wannan ne a siyasance a zaben Afrilu mai zuwa, domin ya kada abokin adawarsa Prabowo Subianto, wanda ake ganin musulmai sun fi son sa.

"Ganin yadda yake samun koma baya, za a iya yarda cewa wannan wani kokari ne na cin kuri'un musulmai masu zabe."

Masu kare Ba'asyir sun musanta cewa matakin "kyauta ne" daga Shugaba Widodo inda aka ce an sake shi a "kyauta ba tare da sanya siyasa ba."

Labarai masu alaka