Faransa da Italiya na cacar baki kan Afirka

Luigi di Maio Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Luigi di Maio ya zargi Faransa da haddasa kwararar 'yan ci-ranin Afirka zuwa Turai

Faransa ta kira jekadiyar Italiya bayan mataimakin Firaministan Italiya Luigi di Maio ya zargi Faransa da ci da gumin Afirka tare da kara rura kwararar 'yan ci-rani.

A ranar Lahadi ne, Luigi di Maio ya yi kira ga Tarayyar Turai ta kakaba takunkumi ga Faransa saboda manufofinta a Afirka.

Ya ce, "har yanzu Faransa ba ta daina mullkin mallaka ba kan kasashen Afirka guda 10."

"Kasashen turai ne suka sa mutane yin kaura, mu samman Faransa da har yanzu ba ta daina yi wa kasashen Afirka mulkin mallaka ba," in ji shi.

Ya kuma ce ba don Afirka ba, da yanzu Faransa tana matsayi na 15 a jerin kasashe masu karfin tattalin arziki maimakon na shida a duniya.

Ya kuma zargi tattalin arzikin Faransa da ci da gumin wasu kasashen Afirka ta hanyar amfani da kudinta na CFA.

Wannan ne ya sa ofishin harakokin wajen Faransa ya kira jekadiyar Italiya Teresa Castald a Paris domin ya ji kokenta da kuma yin karin bayani.

Gwamnatin Italiya ta yanzu dai ta sha yin cacar-baki da Faransa kan 'yan ci-rani da zanga-zanga da kuma al'adu.

Me suke jayayya akai?

Dangantaka tsakanin Faransa da Italiya ta kara tsami ne tun kafa sabuwar gwamnatin Italiya a 2018.

Danganta tsakanin kasashen biyu ta fi tsami ne kan batun 'yan ci-rani. Kasashen biyu na jayayya ne kan yadda Faransa ke taso keyar 'yan ci-rani zuwa kan iyakar Italiya.

Italiya ta zargi Faransa da kin karbar 'yan ci-rani, bayan Faransa ta ce Italiya ba ta taimaka wa masu aikin ceto 'yan ci-ranin a teku.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sama da 'yan ci-rani 4,200 aka ruwaito sun tsallaka zuwa Turai a cikin kwanaki 16 na farkon shekarar 2019

Labarai masu alaka