Kwana 22: Akwai bambanci idan wani ya yi nasara a zaben 2019? #BBCNigeria2019

Buhari da Atiku Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutane a ko da yaushe a Najeriya, hankulansu a lokacin zabe ya fi karkata a kan waye dan takara, maimakon abubuwan da suka damu kasa.

Tunaninsu a ko da yaushe shi ne wane bambanci za a samu a kan dan takara.

Wuse Beggar!Wuse Beggar!! Wuse Beggar!!! Yadda kwandasta a tashar bas ke neman fasinja ke nan.

Motar ita ce tafiya mafi nisa da bas ke yi daga unguwar Maraba da ke jihar Nasarawa zuwa cikin garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Bas din dai na tsayawa ne a tashar Berger, inda kwandasta ya mayar da shi Bega.

A cikin motar fasinjoji akan rinka musu da juna. Yanzu lokaci ne na zagayowar zabe!

A lokacin ne za ka ga babu zancen da ake yi a irin wannan wajen face na 'yan takara.

A yanzu haka akwai 'yan gani kashenin Shugaba Muhammadu Buhari, su kan ce ai mutum ne mai nagarta da aminci kuma ba ya sata.

Su kuwa wasu fasinjojin magoya bayan tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar ne, su kan ce, bisa la'akari da bakar azabar da ake sha a lokacin mulkin Buharin, ai Atiku zai iya fitar da Kasar daga wannan kangi.

Akwai kuma wasu mata da suke goyon bayan tsohuwar mataimakiyar shugaban Bankin Duniya reshen Afirka kuma mai fafutuka Dr Oby Ezekwesili.

Su ana su ganin, babu wanda zai iya shugabancin kasar face ita, su kan ce ai yanzu talauci ya yi wa kasa katutu, ga shi akwai dumbin matasa da ba su da aikin yi yara na mutuwa a asibiti saboda rashin magani, don haka daga Buhari har Atiku babu wanda zai iya tsamo kasar daga wannan kangi sai ita.

Image caption Fela Durotoye na daga cikin 'yan takarar

Akwai dai 'yan takarar shugabancin kasa da dama, wasu ma ba a sansu ba.

Wasunsu sabbi ne a harkar siyasa. Akwai sunayen mutane da dama da suke takarar shugaban kasa a Najeriya, cikinsu akwai Fela Durotoye da Farfesa Kingsley Moghalu da kuma Omoyele Sowore.

Kamar yadda ake musu a bas, ra'ayoyin mutane ya bambanta a game da 'yan takara.

Kusan al'ummar Najeriya miliyan 80 ne suka yi rijista domin kada kuri'unsu a zaben da za a yi a ranar 16 ga watan Fabrairu.

A wuraren yakin neman zabe daban-daban da ake yi a Najeriya, babu abin da zaka rinka ji sai yadda ake ambaton sunayen 'yan takara.

Ga wasu masu kada kuri'a ana ganin kamar a wannan karo ma dai dan takara za su duba ba wai matsalolin da suke damun kasa ba.

Ba wannan ne karon farko ba, mutane sun saba yin haka, illa kalilan da su kan duba ko kuma suka damu da wanda ya cancanci samun nasara.

Mrs Kemi Diego- Okenyodo, kwararriyar mai shari'a' ce a kan masu aikata manyan laifuka ta ce ga mutanen da suke zabe dan dan takara, to an bata su da son kudi.

Ta ce ' Ina ganin yana da kyau idan za mu samu wani dan takara wanda ya ke sabuwar fuska ya lashe zabe.

Tsoffin 'yan takara suna da tasu matsalar. Har yanzu mutane mutum suke dubawa, kuma kudi ma zai takara muhimmiyar rawa.

To amma idan muka samu sabuwar fuska matashi wanda ke da sabbin manufofi, ina ga ya cancanta irin wadannan 'yan takara a rinka barinsu su gwada shugabanci'.

Yakin neman zabe dai, abu ne da 'yan takara ke yi domin yada manufofinsu da kuma yadda za su tafiyar da kasa.

A shekarar 2015, ta kafa tarihi a zaben shekarar a Najeriya a inda dan takarar babbar jam'iyyar adawa ya kayar da shugaba mai ci.

Wani abu da aka yi a lokacin yakin neman zaben wannan shekara, shi ne an mayar da hankali ne a kan 'yan takara.

Najeriya dai na cikin tsakiyar fama da ayyukan masu tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram, wadda za a iya cewa ta mamaye wasu yankuna a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Ta lalata wurare kamar garuruwa da kauyuka a Maiduguri inda a can ne kungiyar ta fi karfi.

A sakamakon ayyukan wannan kungiya, daruruwan mutane sun rasa gidajensu da muhallansu.

Image caption Kingsley Moghulu na daga cikin 'yan takarar

Shalkwatar 'yan sanda da kuma ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriyar, na daga cikin wuraren da 'ya'yan wannan kungiya suka kai wa hari.

Tashar Nyanya, wadda ke wajen birnin Abuja sau biyu kungiyar ta Boko Haram na kai mata hari, inda aka rasa daruruwan rayuka sakamakon hare-haren.

Ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari tsohon soja ne, ana ganin zai iya kawo karshen ayyukan masu ikirarin jhadin wadanda suke barazanar mamaye kasa.

A kan haka ne, ake ganin cewa babu wani kalubale da shugaban zai fuskanta a wannan bangare, inda wasu masu goyon bayansa ma ke cewa ai da ganinsa ma kawai an san babu wata tambaya wajen yakar masu tayar da kayar baya.

Ana kuma cewa Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da amana. Hakan ya sa magoya bayansa suka yi amanna cewa idan har ya zama shugaban kasa to zai bunkasa tattalin arziki da daga darajar kudin kasar.

Mutane sam ba sa la'akari da manufofi da kuma akidar jam'iyyar Shugaba Muhammadu Buharin.

Shi kuwa tsohon shugaban kasar Najeriyar Goodluck Jonathan ana ganinsa mai rauni, ko da yake ma wasu kasashen duniya na yi wa Najeriyar kallon kasar da cin hanci da rashawa ya yi wa katutu.

Irin wadannan 'yan matsaloli ne ya sa a lokacin wancan zaben, mutane suka zabi dan takara, maimakon jam'iyya.

To abin tambayar a nan shi ne, shin ko irin haka za ta faru a zabe mai zuwa?

Dr. Otive Igbuzor, shi ne wanda ya kafa cibiyar wanzar da shugabanci nagari da dabaru, yana ganin cewa duk wanda ya samu nasara a zaben 2019 a Najeriya yana da muhimmanci.

Image caption Obadiah Mailafia ma na takarar shugabancin kasar

Sannan kuma yana da ra'ayin cewa, duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa da wadanda suka samu nasara a zaben majalisun dokoki na jiha da na tarayya, da gwamnoni su ne za su nuna irin gwamnati da kuma manufofin da za a aiwatar.

Ya ce 'Abubuwa na sauyawa a hankali a Najeriya, kuma zaben bana zai kasance hadi ne na zabar dan takara da kuma zabar jam'iyyar da za ta kawo ci gaban kasa'.

Ya ce ana sa ran ganin sakamakon zaben 2019, zai dogara ne a kan manyan abubuwa biyar:

1. Alkawuran da 'yan takara suka yi

2. Halayya da kwarewar 'yan takara

3. Hana sayen kuri'a

4. Wadanda ke kan mulkin na son kare kujerunsu

5. Kariya ga jami'an zabe da kayan zabe da dai sauransu.

Tuni dai aka fara yakin neman zabe a Najeriya.

Manyan jam'iyyun kasar wato APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP, har yanzu suna ta kokari ne na nuna martabar 'yan takararsu.

Jam'iyya mai mulki ta APC, na nuna martabar dan takararta Shugaba Muhammadu Buhari a kan cewa shi mutum ne tsayayye wato kaifi daya ke nan, yayin da ita kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ke cewa dan takarar shugabancin kasarta, babban dan kasuwa ne wanda ya ke da kwarewa a kasuwancinsa, don haka suke ganin zai iya dawo da da tattalin arzikin kasa kan hanya madaidaiciya.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Dr. Ernest Ereke malami ne a Jami'ar Abuja kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa.

Ya ce: "Duk wanda ya yi nasara a zaben nan nauye-nauye da dama za su hau kansa na yadda zai tafiyar da kasar - wacce a yanzu haka take fuskantar matsaloli da suka hada da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin abubuwan more rayuwa da rashin aikin yi da rashin hadin kan kasa da kuma rashin tsarin ilimi mai kyau.

A ganinsa, zabukan ba za su dogara kan matsalolin kasar ba, sai dai kan wasu abubuwa da tun farko aka saba yin su na rashin duba cancantar shugabannin da za a zaba.

"Bambancin da zai yi shi ne 'yan Najeriya suka sake samun damar ko dai su zabi mutanen da za su ciyar da kasra gaba ko kuma su mayar da ita baya.

Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum Husseini Abdu, ya ce wadannan zabukan za su kasance wadanda mutane za su raja'a wajen duba dan takara ne maimakon matsalolin da ake fama da su.

Ya ce: "Tabbas mutum ne mai farin jinin jama'a yayin da shi kuma Atiku yake da rajin farfado da tattalin arziki.

'Yan kasuwa za su fi farin ciki da Atiku maimakon Buhari, tun da shi ya fi nuna zakuwar assasa gwamnatin da za ta duba tattalin arziki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sai dai kuma irin wadannan manyan 'yan kasuwa ba 'yan kasar ba ne, don haka babu wani tasiri da za su yi kan zaben.

A hannu guda kuma Buhari zai fi karfi ne wajen yaki da cin hanci da rashawa, wanda hakan talakawa suka fi so, duk da cewa bangaren adawa na ganin akwai wariya a yaki da cin hancin da ake yi.

Ra'ayoyin mutane sun bambanta. Sai dai mafi yawan 'yan Najeriya sun riga sun mika wuya.

Batun zabukan Najeriya na 2019 yana daukar hankali sosai, musamman saboda 'yan takarar. 'Yan takara ne da suka hada da matasa da tsofaffin mutane.