Hotunan yadda Buhari ya gaisa da Obasanjo

Obasanjo ya gaisa da Buhari Hakkin mallakar hoto Presidency

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gaisa da Buhari bayan wata doguwar wasika da ya rubutawa shugaban.

Buhari da Obasanjo sun gaisa a taron majalisar koli da ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da alkalin alkalai da ake gudanarwa a fadar shugaban kasa.

Wasikar Obasanjo mai yawan shafi 16 ta ja hankali a Najeriya inda Obasanjo ya kwatanta gwamnatin Buhari da irin ta Abacha tare da zargin INEC da shirya magudin zabe.

A martanin da ta mayar, fadar shugaban kasa ta ce tsohon shugaban na bukatar kwararren likita ya duba lafiyarsa, inda ta yi masa fatan samun waraka cikin sauri.

Bayan wasikar kuma Obasanjo ya caccaki Buhari a wata hira da BBC, inda ya ce shugaban yana yaki ne da 'yan adawa tare da gafarta wa masu laifi a APC.

Ya kuma ce ya yafe wa tsohon mataimakinsa Alhaji Atiku Abubakar dan takarar babbar jam'iyyar hammaya ta PDP a zaben 2019.

Sai dai kuma fadar shugaba Buhari ta danganta kalaman na Obasanjo a matsayin wani yunkurin wasu 'yan siyasa da ba za su iya ja da Buhari ba a siyasance sai dai su rika cin dunduniyarsa.

Ga hotunan yadda suka gana

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Wasu sun yi tunanin Obasanjo zai kauracewa taron bayan wasikar da ya rubuta ta caccakar Buhari
Hakkin mallakar hoto Presidency
Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption An gudanar da taron ne ranar Talata
Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan da Shonekan sun halarci taron majalisar
Hakkin mallakar hoto Presidency
Hakkin mallakar hoto Presidency
Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Tsohon shugaban mulkin soja Abdussalam Abubakar ya halarci taron majalisar.